Image

Imam Muhammad Nasir Adam

1.1 DANGANTAKAR SHAIKH IMAM MUHAMMAD NASIR ADAM

Da farko sunan Mahaifinsa Shehu Malam Adamu Ɗan Shehu Muhammadu Jari, Ɗan Shehu Mahmud Bazazzagi Ɗan Shehu Hamid. Sunan mahaifiyar shehu Adamu Khadija, Baki ɗayan su manyan Malamai ne waɗanda suke yiwa addini hidima da Jikin su da lokacin su da Aljihun su.
A wancan lokaci sun kasance suna yawo ƙasashen baƙaƙen fata don yada addinin musulunci a yankin Afrika ta yamma, a lokaci a na kiran yankin da “Bilad Sudan”. Wannan yanki ya haɗa da wani bangare na Arewacin Najeriya, Ƙasar Nijar, Kamaru, Sudan da sauran su. A wancan lokaci turawa ba su a wancan loƙacin kasashen suna dunkule, Turawa basu rarraba suba. Haka waɗannan bayin Allah suka ci gaba da aikin yaɗa addini da ilimantar da al’ummar musulmi, kuma sun yada zango a wurare da dama, sakamakon haka addinin musulunci ya yaɗu a wannan yanki na yammacin Afrika.

1.2 TAKAITACCEN TARIHIN MAHAIFIN SA

dangane da tarihin Mahaifin sa (Shehu Adamu), bayanai ingantattu sun nuna cewar, an haife shi a Shekara ta 1874, kuma ya rasu a shekara ta 1994, wanda ya nuna cewa Shehu Adamu ya rayu a duniya shekaru ɗari da ashirin (120). Kenan.

Shehu Adamu ya rayu da Mata hudu (4) kuma yana da ‘ya’ya ashirin (20), waɗanda suka haɗar da maza goma sha ɗaya (11) da kuma mata tara (9) Ga sunayen su kamar haka:

1.3. ‘YA’YAN SHEHU ADAMU
‘YA’YA MAZA

1. Alh. Rabi’u Adam
2. Alh. Isma’il Adam
3. Malam Iliyasu Adam
4. Alhaji Hamza Adam
5. Malam Muniru Adam
6. Malam Abdullahi Adam
7. Shaikh Imam Muhammad Nasir Adam
8. Malam Mukhtar Adam
9. Malam Hadi Adam
10. Malam Ahmadu Adam
11. Malam Sa’idu Adam

‘YA’YA MATA

1. Hajiya Safiya Adam
2. Malama Rahama Adam
3. Malama Maryam Adam
4. Malama Maimuna Adam
5. Hajiya Aishatu Adam (yar kwari)
6. Malama Halima Adam (hana)
7. Malama Amina Adam
8. Malama Fatima Adam
9. Malama Hindu Adam

Kamar yadda muka saba jin Tarihin manyan Malamai a kan sha’anin neman ilimi, shi ma Shehu Malam Adamu ya yi yawon neman ilimin sa a garuruwa da dama, daga cikin waɗannan garuruwa akwai: Garin Kano, a inda yayi karatu a unguwar magoga wurin Shehu Malam Muhammadu Salga, kuma yana daga cikin manyan almajiran da Malam Muhammadu Salga ya yaye su kuma ya yi musu izinin fara karantarwa, a lokacin Shehu Malam Abdullahi Salga yana yaro, wannan dalili ne ya sa, lokacin da Shehu Abdullahi Salga ya zama Halifan Mahaifin sa (Shehu Malam Muhammadu Salga) yazam yana girmama Shehu Malam Adamu har ya kan tashi ya tafi garin batsari ya zauna a can har kwana bakwai. A waɗansu lokutan ma an ce yakan shiga halwa ta tsawon kwanaki arbain (40) a garin saboda yadda yake ba garin muhimmaci, Mal. Ya’u Zakari aka sami wannan bayani da wurinsa.
    Mal. Kabiru Lirwanu daya daga cikin ɗaliban shehu Adamu yace shehu Adamu ya shaida masa cewa a shekar da zai je aikin hajjin sa ta farko ya yada zango a garin kano wajen malam Muhammadu Salga, a inda ya zauna a wajen sa kafin ya tafi tsawon lokaci yana jin karatu, sai ya yi sha`awar yin karatu a wujen sa idan ya dawo daga hajji. To da yaje makka sai ya tarar da malam Abubakar kusada yana karantarwa sai ya zauna ya yi ta karatu a wajen sa tsawon lokaci, har zuwa lokacin da malam Abubakar kusada ya yi niyyar zai rubuta littafin tafsirin alƙur`ani, amma saboda kusancin sa da malam Adamu sai ya bashi shawara cewar yana ganin tunda akwai malamai da yawa da suka yi talifi akan tafsirin alƙur`ani, shi kuma yana ganin da zai yi sharhin littafin askari, kasancewar litttafin ya samu karbuwa, kuma ba`a da sharhin sa sosai musamman a Najeriya, a ganin sa zai fi amfani ga al`umma. Kuma hakan aka yi a inda malam Abubabakar kusada ya rubuta littafin (sharhin Askari) mai suna ; ``Ashalul masaliki sharhu irshadissaliki``. Littafin juzu`I uku ne (3).
   Sannan shehu Adamu yayi zaman neman ilimi a garin zariya wajen mal. Jibrin Na`iya, ɗaya daga cikin mashahuran Malamai a ƙasar zaria, kuma alokacin da shehu Adamu ya sauke littafin mukhtasar khalil da alfiyya ta Ibn maliki sai malamin ya yi masa izinin da ya koma wajen malam ma`aji isyaku, (shima sanannen malami ne a zariya unguwar kakaki yake) don ya cigaba da karatu a wurin sa, wanda awurin sa ne ya koyi karatun Tasrifi kuma ya kara faɗaɗa karatun sa na Nahwu hakan ta sa ya samu alaƙa da malamai masu yawa a garin zariya. Daga cikin abokan karatun sa a lokacin akwai Mal.Abdulƙadir zariya wanda daga baya shehu Adamu ya aika da ɗaya daga cikin `ya`yan sa (Alh. Hamza) yaje ya yi karatu a wajen Mal. Abdulƙadir zariya, haka nan shehu Adamu yana da alaƙa mai kyau tsakanin sa da shehu yahuza zariya da sauran malamai da dama a garin zariya, musamman lokacin da maulan mu shehu Ibrahim ya bayyana suka yi masa caffa sai alaƙar su ta ƙara ƙarfi, bayan ta yin karatu tare.
   Sannan Shehu Adamu ya zauna a Gusau da shinkafi don aikin yaɗa addini da neman ilimi haka kuma Shehu Adamu yana da gida a garin shinkafi a matsayin sa na ɗaya daga cikin manyan malamai da suka zauna a garin, kuma zamu iya cewa shi ne babban Malamin su wanda har yanzu zuwa wannan lokaci, almajiran sa da almajiran almajiran sa ne suke karantarwa a garin. Bayan garin shinkafi, Shehu Adamu ya zauna a garin Maraɗi, tsawon lokaci, ya karantar da almajirai masu tarin yawa yanzu haka yana da yaya da jikoki a can.
   Daga cikin almajiran sa akwai Alkalin Alkalai na garin Maraɗi wanda ƙanin sa ne, kafin a naɗa Malam idirisu a wannan matsayi sai da aka fara neman Malam Adamu ya amince a naɗa shi wannan mukami, amma bai karɓa ba, sai ya ce``ga kani na nan Malam Idirisu, sai a naɗa shi a madadi na`` kuma hakan aka yi, a inda Mal. Idirisu ya zama Alƙalin Alƙalai na garin maraɗi har tsawon rayuwar sa. Wani abin sha`awa shine yadda shehu Adamu da alkali Idirisu suke girmama junan su, har takai idan shehu Adam ya kai wa alkali Idrisu ziyara a garin maradi sai ya daina yiwa almajiran sa darasu ya koma gefe cikin almajiran sa, shi kuma shehu Adamu sai yahau buzun karantarwar yace da almajiran Bisimillah waye na farko?, idan aka gama biya wa na farko sai na gaba shima ya soma jan baki shehu Adamu yana fassara masa tare cikakken bayani, haka za`ayi ta yi ko tsawon kwana nawa zai yi a garin, alkali baya hawa buzun karantar wa sai shehu Adam ya tafi. Haka nan shima shehu Adamu idan alkali Idrisu ya kai masa ziyara garin batsari baya hawa Buzun sa na karantar wa sai dai alkali Idrisu shine zai bawa almajiran shehu Adamu darasi, shi kuma sai ya koma gefe cikin almajirai kamar yadda alkali Idirisu yake yi masa, ba zai hau buzun karantarwa ba har sai alkali ya tafi. Hakika wannan babbar shaida ce da take nuna kykkyawar alaka da girmamawa a tsakanin su.
   Daga garin maraɗi,shehu Adamu ya zauna ɗan wani lokaci a garin Maiduguri,farlomi, da kuma Sudan. Duk waɗannan garuruwa musamman na Sudan ya yada zango a cikin su ne, yayin da yake kan hanyar sa zuwa aikin hajji, wanda a wancan lokaci ana tafiyar ƙasa, ya karantar da almajirai a waɗannan garuruwa kuma ya haɗu da wasu daga cikin manyan Malamai da yayi karatu a wurin su. Sannan ya zauna a Garin Tara wurin Shehu Malam Jibrin mahaifin Shehu Mal. Abdulmajidu, da sauran su da dama.
   Shehu Adamu kamar yadda tarihi ya nuna ya zauna a Unguwar Malamai wadda take a garin Batsari a jihar Katsina, kuma ya kafa makaranta, wacce a sanadiyyar ta ne Allah ya albarkaci garin, da Jama’a waɗanda mafiya yawan su almajiran sa ne waɗan da suka zo daga garuruwa daban daban kamar; Jibiya, Kaduna, Sokoto, Maraɗi Ƙauran-Namode, da sauran su. Daga cikin manyan almajiran sa akwai Mal. Sulaimanuddaraji, wanda shi ma babban Malami ne kuma limami ne wanda ya zauna a matsayin almajirin Shehu Adamu na tsawon Shekaru arba’in wanda ya kasance yana karatu a gaban sa tare da sauran manyan almajirai. .
   Shehu Adamu yana daga cikin manyan Almajiran Maulan mu Shehu Ibrahim kaulaha na farko farko waɗanda suka ji labarin bayyanar Shehu Ibrahim kuma sukaje suka sadu da shi suka sallama masa tun kafin da’awatul Jafla, kuma ya je Madinatu Kaulaha har sau uku (3), saboda soyayyar sa ga Maulan mu Shehu Ibrahim (R.A), duk da cewa a wancan lokaci tafiye-tafiye irin wannan suna da matuƙar wahala, saboda rashin kyawun hanyoyin sufuri da kuma rashin ababan hawa masu sauri irin waɗan da ake dasu a wannan zamani, amma masu magana suna cewa, garin masoyi baya nisa har ma ya tafi tare da wasu daga cikin Iyalan sa kamar Matar sa Inno da kuma Ɗan sa Alh. Hamza. Haka nan a komawar sa garin kaulaha karo na uku (3) ya tafi tare da Ɗan sa Imam Muhammad Nasir Adam, a shekara ta 1960, ya kai shi ne don yayi karatun addini sannan yayi hidima ga bayin Allah don rayuwar sa tayi albarka, gashi a yau muna ganin sakamakon wannan kyakkyawar niyya da Shehu Malam Adam yake da ita a kan yayan sa Allah ya cika masa burin sa. A nan a kwai darasi mai girma wanda zamu ga muhimmancin zabawa ‘ya’ya Makaranta sahihiya tare da ingantattun Malamai. Domin makomar ‘ya’yan ka shine babban abin alfaharin ka fiye da komai, da fatan Allah ya bamu albarkacin masu albarka Amin.
   Kamar yadda aka bayyana a baya cewa Shehu Mal. Adamu Batijjane ne, kuma ɗaya daga cikin manyan almajiran Maulan mu Shehu Ibrahim na farko da suka sadu da shi a garin Madinatu Kaulaha, hakan ta sa Shehu Malam Adamu ya bada gagarimar gudummawa wajen yaɗa ɗariƙar Tijjaniya, a sanadiyyar haka, ake kiran karamar hukumar Batsari da hedikwatar faira ta Jihar Katsina A wancan lokaci gidan sa ya kasance matattarar zakirai da ma abota salatin Dala’ilu,Ishiriniya,diwani, alburda da sauran manyan litattafan madahu, musamman a ranar Juma’a wacce rana ce da zakirai su ke rako shi gida su kafa da’irar zikiri a cikin wata rumfar ciyawa (wacce ake cewa dabi), sannan idan yamma ta yi a kafa da’irar wazifa da zikirin Juma’a. Sannan a lokacin Maulidi, shehu Malam Adamu baya zama gida saboda hidimar Maulidai.
   A ɓangaren alaƙar sa da sauran Malaman gari zamu iya cewa akwai kyakkyawar alaƙa da fahimtar juna a tsakaninsa da su, duk da cewa a wannan lokaci shi ne Babban Malamin garin wanda babu sama da shi, daga shi sai Limamin garin Liman Muhammadu wanda shi ne ya ke kula da Limancin Sallar Juma’a da sauran salloli biyar na kullum, a inda shi kuma Shehu Mal. Adamu ya jiɓinci sha’anin karantar wa da harkar ɗariƙa da wa’azantar wa da sauran su. Wannan ta sa an samu kyakkyawan yanayin zamantakewa a tsakanin su, sakamakon kowa ya tsaya a kan aikin sa (wani baya shiga aikin wani). Har yau dinnan zawiyyar Shehu Adamu anan kowa yake zuwa zikirin juma a.

1.4. WASU DAGA CIKIN MANYAN ALMAJIRAN SHEHU ADAMU

1-Mal. Ali Usudu
2- Mal. Ahmad Zaure
3- Liman Mal. Ahmadu (Limamin Batsari)
4- Mal. Sulaimanuddaraji
5- Mal.Audu Na Mashi
6- Mal.Awaisu makaranci
7- Mal.Usamatu Alaramma
8- Mal. Ahmadu Zakka
9- Mal.Mamman Godo
10- Mal.Ammani Watan Godiya
11- Mal.Alh. Mamman Yasoni
12- Mal.Muhammadu masha yabo kamba
13- Mal. Iyal Katsina
14- Mal. Dan juma Katsina
15- Mal. Lawal Saho
16- Mal. Abdulkadir Makaranci
17- Mal. Mai-Shanu
18- Mal.Sagiru Gafai
19- Mal.Lauwali Ɗan-Geza
20- Mal.Idi Mijin Hani
21- Mal.Abu Kandawa
22- Malam tadudu
A takaice wannan shine ɗan abin da aka iya ciro wa daga cikin tarihin Shehu Malam Adamu, da fatan Allah ya sa mu amfana daga abin da muka ji na darussan da ke kunshe a cikin tarihin sa.

HAJIYA HALIMA ‘YAR LIMAN TINAU Jibiyar Maje (1888 – 2018)
Mahaifiyar Shaikh Imam Muhammad Nasir Adam

Ta ɓangaren mahaifiyar Imam Muhammad Nasir Adam sunan ta Hajiya Halima Abubakar Liman tinau, kuma ita ma ta fito daga babban gida mahaifinta shine limamin garin Jibiya (Liman Abubakar tinau), wanda ya kasance mutum ne mai rufin asiri ga kyauta da son ciyarwa, gidan sa a kowane lokaci akan samu an tanadi fura saboda saukar baƙi domin a wancan lokacin ita ce abincin da aka fi saukar baƙi da ita,

kuma daga cikin baiwar da Allah ya yi masa shi ne wannan fura ba ta ƙare wa a gidan sa har takai mutanen garin su na ganin cewa rashin rabo ne babba ace mutum ya zo gidan Liman baƙunta kuma bai sha fura ba. A taƙaice dai wannan yana nuna mana irin Nagartar da Liman Tinau yake da ita da kuma tarin abubuwan alkairan da ya shuka kuma wannan dalili yasa Allah ya bashi zuriya ta gari.

    Malam Muhammad Nasir Adam ya samu tarbiyya da kulawa sosai daga wurin mahaifiyar sa Kuma ta tsaya tsayin daka wajen nuna masa mahimmancin karatu da koya masa kyawawan dabi’u ba tare da nuna masa so da shagwaba wadda zata hana ta yi masa hukunci ba. Shima Malam a tarihin zaman sa da mahaifiyar sa bai taɓa yin wani abu wanda mahaifiyar sa ta yi fushi da shi ba domin tun yana ƙaramin yaro ta saita shi akan kaucewa duk waɗan su ɗabi’u da basu da kyau. Daga cikin misalai na waɗan su abubuwa da suka faru tsakanin sa da mahafiyar sa a lokacin yana cikin shekarun ƙuruciya, a kwai wani lokaci da ta gan shi a gida yana rubutun sha, har lokacin Makaranta ya yi bai tashi ya tafi ba, sai tayi masa magana tace “ka tashi ka tafi Makaranta lokaci yayi” sai ya amsa mata, kuma ya cigaba da rubutun sa, yana so har sai ya ƙarasa sannan zai tashi ya tafi, ganin lokaci yana tafiya bai tashi ya tafi ba sai ta kara yi masa magana, shi kuma a lokacin ya kusa ƙarasawa, sai yayi mata shiru bai ce da ita komai ba, ya cigaba da rubutun, ganin haka ya sa ta taso da sauri ta taho kan sa, ganin haka sai ya yar da allon ya gudu saboda fushin da yaga tayi yaje ya tsaya a bakin kofa, ita kuma ta ɗauki allon ta jefo masa har ya ji masa ciwo a gefen karamin ɗan yatsansa na hannu, wanda wannan tabo har yanzu yana nan a hannun Malam kuma daga wannan rana Malam bai sake zama a gida yana yin wani abu ba alhalin lokacin Makaranta yayi, a nan zamu iya cewa horon da ta yi masa ya sa ya gane cewa karatu ba abin wasa bane, wanda hakan yasa tun yana da kananan shekaru ya fahimci cewar karatu abu ne mai matuƙar muhimmanci wanda bai kamata a yi wasa da shi ba. A nan lallai a kwai abin kwaikwayo musamman ga iyaye mata na wannan zamani waɗanda suke so yayan su su sami ingantaccen ilimi da tarbiyya ta gari. Haka nan daga cikin gudummawar da mahaifiyar sa ta bashi wajen sama masa albarka, ta kasance tana aunar hatsi ta haɗa da ɗan kuɗi ta je ta kai wa Malamar da ta ke koya masa karatu tace “wannan ayi wa Nasiru addu’a” sannan bugu da ƙari ta ba shi gudummawa wajen tarbiyyantar da shi a kan gaskiya da riƙon amana, a inda a kwai wani lokaci wanda mahaifin sa Shehu Malam Adamu ya aike shi da kuɗi ( kwabo biyu) ya siyo masa nono na ahu, bayan ya siyo sai canjin mahaifin sa ya kama sisin kwabo, to a wancan lokaci saboda ƙuruciya, daga kasuwar bai dawo gida ba sai ya tafi gidan wan sa Alh. Isma’ila, ya cigaba da harkokin sa har mai kosai ta kawo talla, kuma ya yi sha’awar wannan kosan, ya ɗauki wannan canjin ya sayi kosan da su, ganin haka sai Matar wansa (Safiya) ta aika aka a gaya wa Shehu Malam Adamu abin da ya faru, da jin haka sai yace “a gaya wa mahaifiyar Nasiru abin da ya faru,” da taji haka sai ta aika aka kira shi, ta kama shi ta ɗauko wuƙa,(kujigi) mutane suka ta so suna cewa meza ki yi masa? tace “yanka shi zan yi shi kuma yana kuka, yana ƙara, amma duk da haka bata sake shi ba, sai da ƙyar matan gida suka kwace, shi amma duk da haka, ba ta nuna masa ta haƙura ba, in an ƙwace shi sai ta sake kamo shi tana yi masa barazana, tana cewa “sai na yanka shi, yau zai gaya min dalilin da ya sa zai kashe kuɗin mutane, kuɗin da ba nasa ba,`` har dai da ƙyar aka fitar da shi waje yana kuka, wannan ya nuna a zahiri cewa amana ba’a ɗaukan ta a ƙasa sai an yi ƙoƙari matuƙa wajen ɗora yara akan kiyaye ta, ba tare da nuna musu soyayya ba, wanda irin wannan yana tasiri matuka a kan yaro, kuma irin wannan jajircewa da mahaifiyar Malam tayi wajen nuna masa munin dabi’un da basu da kyau tare da ɗora shi akan kyawawan ɗabi’u tun yana da ƙarancin shekaru, hakika yayi masa tasiri, domin a yau da wuya ka samu wani ya zo maka da kuka akan Malam dangane da abin da ya shafi amana ko Ha’inci ko rashin gaskiya, saboda ya horu.
    Daga karshe idan muka dubi nasabar Malam ta bangaren mahaifin sa muka haɗa ta da nasabar sa ta bangaren mahaifiyar sa, zamu ga cewa ba abin mamaki ba ne idan suka samar da nagartattun zuri’a irin wannan domin cewa shi asali naso yake yi.

1.5. SAƁANI A TARIHI SANANNAN ABU NE, HUJJOJIN CEWA SHEHU ADAMU YA YI KARATU A WAJEN SHAIKH MALAM MUHAMMAD SALGA KANO;

1-Bayanan da suka gabata daga Mal. Kabiru Lurwanu sun bayyana cewa shehu Adamu ya zauna a kano wurin malam na salga a lokacin yana kan hanyar sa ta tafiya aikin hajjin sa ta farko na wani lokaci, wannan ba zai hana bayan dawowar sa daga aikin hajji ya zama ya iya zuwa yayi karatu wajen malam salga ba,saboda akwai yalwataccen lokaci da zai iya yin hakan .
2- Shaikh Malam Mahmud salga ɗan Malam salga, an kawo masa wani littafi wanda Mal. Usman ya rubuta akan shehu malam Muhammadu Salga, sai ya ce a kai wa Imam Mal. Muhammad Nasir Adam don ya duba ya yi gyare gyare a kai, bayan sun gama duba littafin shi da Mal. Usman (marubucin littafin), bayan sun kammala suka kai masa ya duba, sai yace bai ga sunan shehu Adamu a cikin manyan almajiran malam Muhammadu salga da aka lissafa a cikin littafin ba, don haka a koma saka shi aciki, wannan dalili ne yasa ga duk wanda ya karanta littafin zai ga sunan mal. Adamu Batsari shi ne ƙarshen rubuta wa a jerin sunayen almajiran Malam Salga.
3- Hujja ta uku, ita ce a shekarar da Imam Muhammad Nasir Adam ya dawo daga Madinatu Kaulaha 1974, bayan sun gama gaisawa da mahaifin sa sai ya shaida masa cewa mal. Mudi salga ya zo ya ce in ka zo yana son ganin ka, bayan yaje garin kano ya sami mal. Mudi sun tattauna sai ya dawo yake shaida wa mahaifin sa cewar mal. Mudi ya nemi da zai ba shi jagorancin makarantar su da suka gina ta a unguwar gwammaja kukar yan caca a karkashin Munalzamatu fitiyanul Islam ta kasa a Kano. Amma shi baya sha`awar fara koyar wa yanzu, shi karatu yake so ya cigaba, sai Shehu Adamu yace da shi ``Ai Ɗan malami na ba zai nemi abu a waje na ba, kuma ina da shi na hana shi, daga nan malam ya ajiye ra`ayin sa ya taho kano a shekara ta 1974.
4- A lokacin da Imam malam Muhammadu Nasiru Adam ya gama makarantar horas da malamai ta katsina (ATC Katsina), sai sharif Abba Abu ya gina masa gida kusa da nasa ya ya ce yazo ya zauna kusa da shi, sai malam yace ya gode amma a fara tambayar izinin mal. Mudi salga, amma ganin kusancin da yake da shi a wurin shehu Adamu sai ya tafi kai tsaye wajen sa, amma bai bada wannan dama ba, duk da cewar shi ma Abba Abu jikan Gatarin baki ne (wani mashahurin malami da shehu Adamu ya yi karatu a wajen sa, sai yace ``ai ɗan malami na ya riga yazo ya tambaye ni, na amsa masa kuma in aka yi Magana irin wannan ba`a warware ta``.
5-Mal. Namadi almajirin Shehu Adamu ya gaya wa Malam cewa ; Shehu Adamu ya gaya masa cewar ya yi karatu tare da su Mal. Shehu Mal. Tijjani Usman Zangon bare bari da Shehu Mal. Atiku Sanka da Shehu Mal. Sani kafinga da Shehu mai hula, amma a lokacin su wadannan Shehunnan matasa ne (basu kai Shehu Adamu shekaru ba)
6-Malam Abdulmajidi daya ne daga cikin almajiran Shehu Muhammadu Salga, shi ma ya bayyana cewa Shehu Adamu ya yi karatu a wajen Malam Muhammadu Salga. Wadannan sun isa hujjoji da za su kara tabbatar mana da cewar Shehu Adamu ya yi karatu a wurin Malam Muhammadu Salga. Da fatan Allah ya ji ƙan su, ya yi musu gafara.

2.1 HAIHUWAR SA DA NEMAN ILIMIN SA

Bayanai na tarihi sun nuna cewar an haifi Malam Muhammad Nasir Adam a shekarar da aka yi gobarar sinima ta Kano, wannan gobara an yi ta ne a shekara ta 1950, saboda haka binciken da na yi ya nuna cewar an haife shi ne a ranar ɗaya ga watan Maris shekara ta 1950 (1/3/1950), a gidan mahaifin sa wanda yake a unguwar malamai garin Batsari, jihar Katsina. Kuma ya tashi a gaban mahaifan sa har ya kai lokacin da ya isa fara zuwa makaranta, a inda ya fara koyon karatu daga gida, a wurin mahaifin sa, kuma ya kasance tun yana da waɗannan ƙananan shekaru ba’a nuna masa komai ba sai karatu, wanda shi ne abinda ya taso ya ga ana yi a gidansu. Dama Hausawa na cewa; kowanne tsuntsu kukan gidansu yake yi, don haka kukan gidan su Malam shine karatu, wannan dalili ne ya sa akasarin abokanan sa sune abokanan karatun sa da wadanda suka taso a unguwa daya, kamar haka;

2.2. ABOKANAN MALAM TUN TASOWA

1-Malam Kasimu M. Abduikadir Batsari
2-Malam Ishka Unguwar Liman
3-Alh. Hussaini Jibo
4-Mal. Iliya Lawan Gafai
5-Mal. Akilu na Malam Ahmadu Babarbare
6-Abdulhamid (Matin jaji/ kurman jaji)
7-Sani na Dan Bilki
8-Yaiya na Malam Uwaisu
9-Iro mai nama
10-Audu Buzu
11-Audu Soja
12-Rabe Unguwar Zamfarawa
Malam bai jima sosai a gida ba, saboda ɗaukar sa da mahaifin sa ya yi, ya kai shi garin Dankar don yin karatun Allo a wajen Mal.Umaru dan Mai. Ɗan bande

2.3 FARA KARATUN SA NA ALLO

Kamar yadda muka sani cewar malam ya fara karatun Allo a gida wurin mahaifin sa da wani malami ana kiran shi Mal. Abdulƙadir. Kuma bayan ya fara sanin baƙi sai mahaifin sa ya ɗauke shi daga gaban sa ya kai shi garin Dankar wanda yake a jihar Katsina a shekara ta 1956. A wancan lokaci, malam yana da ƙarancin shekaru, wannan ta sa karatun ya canza masa domin a wannan yanayi ya kasance yana kewar gida, sannan ya fara fuskantar ƙalubale na canjin rayuwa a cikin sha’anin neman ilimin sa, daga cikin irin waɗannan ƙalubalen da ya gamu da su, sun haɗar da rashin abinci inda, sai sun je sun yi bara sannan za su samu, a lokuta da dama ko sun je sun yi barar an ba su abincin ba su ne su ke ci ba, ana samun daga cikin gardawan almajirai da suke tsayawa a waje da sun ga yaro ya shiga gida ya yi bara an ba shi abinci, sai su ƙwace su cinye, idan kuma ya ɓuya a soro ya cinye ko a cikin gida, sai su shin-shina hannun sa, in sun ji ƙanshin miya, a wannan rana yaro sai ya gwammace da ma bai ci abincin ba, don sai sun dake shi da kwano, banda matsalar rashin abinci akwai, matsalar rashin suturar kirki da wadataccen ruwa, wanda ba sa samun damar yin wanka da wanki akai-akai, sannan ga matsalar wajen kwana, wanda soro ne suke kwana a ciki, idan lokacin sanyi ya zo ba su da abin rufa na kirki, haka a lokacin zafi ga sauro da tsutsa da kuɗin cizo da sauransu. Amma duk da wannan yanayi ba su fasa karatun ba, sai ma abin da ya ƙaru domin a yadda aka ɗora shi a gida, ya san cewar yadda ya zamo masa wajibi ya ci abinci haka ya zamo masa wajibi ya yi karatu, don haka ya ci gaba da haƙuri a cikin halin neman ilimi har zuwa lokacin da Allah ya kawo ƙarshen zaman sa a garin,a shekara ta 1957, lokacin da ɗan uwan kishiyar mahaifiyar sa mai suna ``Gado`` ya tafi da shi Katsina ƙofar ‘yan ɗaka a lokacin allon sa yana (Suratul Asri) kuma yayi karatu ne a wurin Mal. Ali bagobiri wanda shi ne mijin Inna Hafsatu wadda ita ma ta koyar da malam karatu, kuma ita ce take yi masa rubutu a allon sa, wannan mata ta taka rawa sosai wajen ƙarawa malam ƙwarin gwiwa kasancewar sa tun a wancan lokaci yaro ne mai ƙwazo matuƙa da gaske, haka nan kuma itace matar malamin su wadda mahaifiyar malam take aikawa da hatsi da ‘yan kuɗi tace a yi wa Nasiru addu’a.
     Wannan ya na farantawa malamin sa kuma ya sa, ya tabbatar da cewar iyayen Muhammad Nasir suna da kulawa sannan kuma suna yabawa da abin da ake koya masa na karatu da tarbiyya.
     Malam ya zauna tsawon lokaci a Katsina (ƙofar ‘yan daka) kuma karatun sa ya yi nisa har ya yi sauka, amma bai kai ga haɗa wa ba, a lokacin ne mahaifin sa zai koma garin Madinatu Kaulaha komawa ta uku, a inda ya tafi da shi a shekarar 1960, kuma ya kai shi ne don ya cigaba da karatun sa a can, Malam ya cigaba da zama a garin Madinatu Kaulaha cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.

2.4 TSARIN GARIN MADINATU KAULAHA DA ƊABI’UN MUTANEN GARIN
     Garin Madinatu Kaulaha ɗaya ne daga cikin fitattun garuruwan ƙasar Sinigal, Ita kuma ƙasar Sinigal ɗayace daga cikin ƙasashen yammacin Afrika, sannan ita ce ƙasa ta ƙarshe wadda daga ita babu wata ƙasa a yammacin Afrika sai Teku.
     A dangane da asalin garin madinatu kaulaha, gari ne wanda maulan mu shehi Ibrahim ya kafa shi a gefen garin kaulaha, kuma ya kira shi da suna (Madinatu Kaulaha), wanda ya kasance wuri ne da ya keɓe, shi da almajiran sa yana koyar da su karatu da koya musu yadda ake wa’azi da koyarwa don yaɗa addinin Musulunci kuma Allah ya karɓi wannan kyakkyawar niyya tasa, a inda a yau wannan makaranta ta bunƙasa, kuma ɗalibai daga ko ina a duniya suna zuwa don yin karatu, kuma tana ƙara samun cigaba yadda ya kamata ƙarƙashin kyakkyawan tsarin da maulan mu Shehu Ibrahim ya ɗora ta a kai. 2.5 TSARIN MAKARANTAR MAULAN MU SHEHU IBRAHIM NYASS (RTA)
     Kamar yadda muka faɗa Madinatu Kaulaha gari ne wanda maulan mu Shehu Ibrahim ya kafa kuma Allah ya albarkaci wajen har ya zama babban gari. A dangane da yadda tsarin makarantar shehu take, za mu iya cewa tsari ne irin na karatun soro, kuma makaranta ce ta haddar al-ƙur’ani da karatun sauran litattafan addinin Musulunci (na shari’a da sunna muhammadiyya da kuma ilimin larafci), kuma a wancan lokaci da maulan mu Shehu Ibrahim ya kafa makarantar shi kaɗai ne yake koyar da almajiran sa, ba shi da mataimaki, wanda zai dinga yi wa almajiran sa bitar karatun su, kuma babu wani wanda zai gyara musu allon su sai daga baya bayan ya yaye wasu daga cikin almajiran sa, sai ya ɗora su a kan waɗansu fannoni suna rage masa aiki. Daga baya, bayan al’amura sun sake bunƙasa na sha’anin hidimomi da ɗawainiya sai ya kasance yana koyar da manyan almajiransa wasu daga cikin manyan littattafai kamar Tafsiri da Muƙamatul Hariri da sauran su. Da hidima ta ƙara yin yawa, ƙasashen duniya a wancan lokaci suna buƙatar saduwa da Shehu kuma al’amuran yaɗa addinin Musulunci da saita al’ummar Musulmi a kan hanya madaidaiciya (Ɗariƙa), su na ƙara bunƙasa sai ya zamto shehu ya buɗewa waɗansu daga cikin manyan almajiran sa makarantu, saboda su cigaba da koyar da almajirai. Daga cikin makarantun da maulan mu Shehu Ibrahim ya kafa a garin Madinatu Kaulaha akwai; makarantar Tsoho Ahmadu Cam, da Makarantar Sayyidi Aliyu Sise wadda a wannan makaranta ne Imam Muhammad Nasir Adam ya yi karatu yayin zaman sa a madinatu kaulaha, sannan sai makarantar sayyida Ruƙayyat Nyass, da makarantar Kabiru Fai, da makarantar Barhama Jof sai makarantar Mal. Musa Maraɗi wanda shikuma sayyidi Aliyu Sise ne ya bashi damar ya dinga karantar da almajirai Hausawa domin su fahimci karatu yadda ya kamata, sai Shehu Malam Lauwali Jega shi ma malami ne da yake karantar da ‘ya’yan Hausawa a masallaci, daga cikin ‘ya’yan wannan malami, akwai Abdullahi wanda ya kasance aboki sosai ga malam wanda ta su ta zo ɗaya kuma sa’annine wanda shi Abdullahi, Allah ya yi masa rasuwa tun ana madinatu Kaulaha da fatan Allah ya ji ƙansa amin.
     Waɗannan makarantu da maulan mu Shehu Ibrahim ya kafa, a da ba a bayar da Shahada ga waɗanda suka gama ta, saboda a lokaicn ana kan tsari ne na karatun soro, amma a yanzu an zamanantar da su, a inda ake bayar da shahada ga waɗanda suka fita daga makarantun, kuma tarihi ya nuna cewar maulan mu shehu Ibrahim ya ɗaukar wa mahaifin sa alƙawari akan cewar zai tsaya iya ƙoƙarin sa don yaga cewar makarantar da ya kafa (ta Ma’ahad Ash-Sheikh Abdullahi Nyass) bata mutu ba saboda shuɗewar lokutai, wannan dalili ne ya sa maulan mu Shehu Ibrahim ya ga dacewar yiwa wannan makaranta tsari ingantacce wanda zai dinga tafiya da zamani, don haka sai ya aika ƙasar misira wajen Shehu Naziru (Ɗansa), a inda ya buƙaci da ya dawo gida don ya ɗora shi a kan harkar tafiyar da wannan makaranta. Bayan Shehu Naziru ya dawo sai ya fara da horar da manyan almajiran Shehu yadda ake koyarwa tare da yin da’awa kasancewar suna da karatu yadda ya kamata, bayan ɗan wani lokaci sai aka tura su gari-gari don su je su karantar kuma su cigaba da yaɗa Addinin Musulunci a sauran wurare. Waɗannan Malamai sukan yi wata tara suna koyarwa a garuruwan da aka aika su kafin lokacin damina, a wannan lokaci ne sukan dawo saboda aikin gona wanda almajirai ne suke yi a wannan lokaci kuma wannan ma yana ɗaya daga cikin tsarin da ya tabbatar da ɗorewar wannan makaranta.
     Banda wannan, Shehu Nazir ya ƙara zamanantar da tsarin makarantar a inda ya yi mata tsari na firamare da sakandire (ƙarama da Babba), wanda har zuwa wannan lokaci makarantar tana ƙara samun cigaba, kuma ana fatan wata rana ta samu cigaba har ta kai matsayin babbar makarantar gaba da sakandire, har ma ta kai matsayin Jami’a da yarda Allah.
2.6 ZAMAN MALAM A MADINATU KAULAHA
     Kamar yadda muka faɗa a baya cewa mahaifin malam (Shehu Malam Adam) yana daga cikin manyan almajiran maulan mu Shehu Ibrahim na farko farko waɗanda suka je, suka sadu da shehu kuma suka sallama masa.
     Amma ɗan sa wanda ya kai garin Madinatu Kaulaha a komawar sa ta ƙarshe shi ne; Imam Muhammad Nasir Adam wanda ya kai shi a shekara ta 1960, kuma a wannan lokaci shehu malam Adamu ya kai dan sa (imam muhammad Nasir) ya zauna a garin na tsawon shekaru uku (3), sannan ya dawo gida a shera ta 1967 sannan ya sake koma wa shi kadai a shekara ta 1968, a inda ya cigaba da ɗaukar karatu a wurin malaman sa na wannan gari na Kaulaha.
     Daga cikin malaman da suka koyar da shi akwai Malam Musa Maraɗi, wanda shi ne malamin da ya fara koya masa karatu a Madinatu Kaulaha, kamar yadda muka faɗa a baya, shi wannan malami shi ne wanda yake koyar da ‘ya’yan hausawa a garin, sannan ya yi karatu a wurin shehu Barhama Job, abokanan sa waɗanda suka yi karatu tare a wurin shehu barhama Job, sun haɗar da; Mal. Zakari zuga, Usman Zugu, Malam Yusuf mai Littafi (wanda yake yiwa maulan mu Shehu Ibrahim aikin bangon litattafan sa, wanda mutumin gana ne). Daga nan malam ya yi karatu a wurin maulan mu Shehu Ibrahim a inda Shehu yake bada karatu a gidan sa da kuma masallaci. Sannan malam ya yi karatu a wurin sayyidi Aliyu Sise, wanda duk da kasancewar a ƙa’idar sayyidi Aliyu Sise baya koyar da ‘ya’yan Hausawa, amma saboda shi malam a lokacin an siya masa keken shanu na aikin gona, sai hakan ta sa ba ya samun damar zama karatu da safe, sai da yamma lokacin da Sayyidi Aliyu Sise ya ke koyarwa, don haka malam ya zama ɗaya daga cikin almajiran sa.
     Daga cikin waɗanda suka yi karatu tare da Malam a gaban Sayyidi Aliyu Sise sun haɗar da; Sayyadi Bashir Sheikh Tijani Usman wanda ya zo a lokacin malam ya yi nisa a karatu gaban sayyidi Aliyu Sise, sannan malam ya yi karatu a wurin Malam Hassan Shafi’u (mutumin Sudan), kuma Allah ya ba shi ilimi da wayewa irin ta zamani da kuma kaifin basira yadda ya kamata. Waɗannan su na daga cikin malaman da malam ya yi karatu a wurin su a garin Madinatu Kaulaha.
     A zaman da ya yi a fadagarin ya yi ƙwazo matuƙa a kan karatu, kuma ya yi ƙoƙari yadda ya kamata a kan hidimta wa makaranta da masallaci, a sanadiyyar haka, ya samu yabo da ɗaukaka daga cikin ɗalibai da suke karatu tare da shi, kuma ya kasance yana da naci akan karatu, wanda idan aka biya masa, sai yayi ta maimaita shi har sai ya tabbatar ya zauna a ƙwaƙwalwar sa, sannan bai damu da yawan shiga hira tare da abokai ba, sai dai in za su yi bitar karatu ko wata tattaunawa ta Ilimi ko sha’anin ƙungiyoyin da suka kafa akan kula da masallaci da tsaftace shi da sauran su.
     Kamar yadda muka a baya cewar Imam Muhammad Nasir Adam ya zauna ne a gidan Sayyidi Aliyu Sise, ya kuma yi gwagwarmayar ƙungiyoyi da sauran al’amura na hidima ga addini daban daban. Daga cikin waɗannan ƙungiyoyi da suka kafa akwai ƙungiyar Ansarul Masjidi, wadda yake a matayin sakataren ƙungiyar, kuma sun kafa ta don aikin kula da masallacin maulan mu Shehu Ibrahim, a inda Mal. Mahmud mai tarihi yake shugabantar ta kuma Mal. Abubakar Mai gafaka yake a matsayin ma’ajin ƙungiya. Banda wannan, malam ya zama mataimakin shugaban ƙungiyar ɗaliban makarantar sayyidi Aliyu Sise, wanda aikin wannan ƙungiya shi ne horar da juna yadda ake shirya huɗuba sahihiya a cikin harshen larafci, wanda a duk sati kowa a cikin su zai shiryo, ta sa huɗubar ya rubuta ta, sannan ya gabatar da ita a gaban sauran ɗalibai, idan an ji kuskure, sai a yiwa mutum gyara. Wannan ya yi matuƙar taimaka musu musamman wajen ƙwarewa a harshen larafci tare da samun gogewa wajen iya gabatar da jawabi gaban jama’a ba tare da shayi ba. bayan wannan malam ya shiga cikin sha’anin koyon karatun tangimi a karan-kansa da koyawa kansa ƙira’ar Sheikh Abdulbasiɗ Abdussamad, wanda a sakamakon haka ne, malam ya yi ƙoƙarin ya koyi kiran sallah irin na larabawa, a inda ya yi wa kansa horo na musamman har yake iya kwaikwayon muryar Sheikh Nazeer Nyass, wanda shi ne wanda yake kiran sallar Asuba kira na biyu (Assalatu khairun minan naumi), amma wannan kiran sallar na Asuba a da ba Shehu Naziru ne yake yi ba, sarkin Madinatu Kaulaha ne yake yi, kafin tsufa ya kama shi a inda maulan mu shehu Ibrahim ya umarci Shehu Nazir ya cigaba sannan shine (Shehu Nazir) yake yin kiran sallah ranar Juma’a bayan Shehu Ibrahim ya zauna a kan mumbarin huɗuba, a inda wani bawan Allah ana cewa da shi carno jallo, shi ne wanda yake kiran sallar farko kafin maulan shehu Ibrahim ya fito.
     Wata rana malam ya shiga Halwa a Masallaci, wanda ya kai shi har ranar Juma’a, yana zaune lokacin maulan mu Shehu Ibrahim yana gab da shigowa masallaci, don gabatar da huɗuba da sallar Juma’a, sai malam ya ga hankalin wannan ladanin ya tashi, yana ta kaiwa da komowa, sai malam ya tambaye shi, “me ya faru naga hankalinka ya tashi haka” sai yake gaya wa malam cewar “Sauran ‘yan mintuna ƙalilan Shehu ya shigo masallaci, amma yaran nan (Bay yaseen) bayan ya san shi ne yake kiran sallah in Shehu ya shigo, ka ga har yanzu bai shigo ba yanzu saboda Allah wannan ya yi daidai kenan? Da malam ya ji haka sai yace masa “Ka kwantar da hankalin ka, in dai kiran sallah ka ke so ni zan yi maka”, da carno jallo ya ji haka, sai ya ji daɗi a ransa amma duk da haka yana kokwanto har yake ƙara tambayar malam, cewar ``yanzu kai ka tabbatar in shehu ya zauna kan mumbari zaka iya tsayawa a gaban sa ka kira sallah``? Malam ya ƙara tabbatar masa cewar ``ƙwarai ma kuwa zan iya``, sai carno yace da malam ya ƙarasa gaba kan shimfiɗar shehu Nazir Nyass ya zauna, bayan maulanmu Shehu Ibrahim ya shigo Masallaci ya zauna, sai Malam ya tashi tsaye ya rangaɗa kiran sallah, Shehu Ibrahim da sauran mutane da suke masallacin suka yi mamakin yadda malam yai kiran sallar kamar Shehu Nazir ne yake yi, abin ya ƙayatar da al’umma har da shi kansa maulan mu shehu Ibrahim, amma, a wannan lokaci shehu bai ce komai ba, ya gabatar da huɗuba kuma ya ja sallah shi kuma ya yi ladanci kamar yadda Shehu Nazir yake yi.
    Bayan Shehu Naziru ya dawo daga tafiyar da yayi sai ya samu labarin cewar akwai wani yaro ɗan Hausawa, ana cewa da shi Muhammad Nasir Adam, ya iya kiran sallah kamar yadda shi Shehu Nazir ɗin yake yi, kuma shi ne yake yin kiran sallah idan baya nan. Da ya ji haka sai ya sa aka kira Imam Muhammad Nasir Adam, yake tambayar sa, a ina ya koyi kiran sallah haka abin sha’awa, sai malam ya ce da shi “ai yadda ka ke yi ne, ni ma nake ji, kuma har na yi wa kaina horo na musamman har sai da na iya, da Shehu Nazir ya ji haka sai ya ce da shi to yayi kyau, kuma abin da nake so da kai, daga yau duk lokacin da na yi tafiya, ka dinga zuwa kana kiran sallah a madadi na ranar Juma’a, sannan da Asuba ka dinga yin kiran sallah na biyu (Assalatu), sai malam yace, ai shi ba zai iya wannan aiki ba ba tare da amincewar Malamin sa ba, wato (Sayyidi Aliyu Sise), to a wannan lokaci, Shehu naziru ya je ya samu Sayyidi Aliyu Sise ya ce da shi, “to ga yadda muka yi da almajirin ka, amma ya ce sai ka yi masa izini” to a wannan lokaci ne Sayyidi Aliyu Sise ya kira Malam ya yi masa izinin yin kiran sallah a masallacin kamar yadda Shehu Naziru ya nema. Kuma haka aka yi har ma saboda yadda yake kwaikwayon muryar Shehu Nazir a wurin kiran sallah, ya sa maulan mu shehu Ibrahim yake kiran sa da “Nazeer” maimakon sunan sa na Muhammad Nasiru, sannan idan ya kira sallar, carno jallo shine ladanin masallacin shehu a madinatu kaulaha wanda a yanzu haka `ya`yan sa ne ladanan masallacin (gwarko da bayi jallo). Da fatan Allah ya bamu albarkar masu albarka Amin.
    Bayan hidimar masallaci malam ya yi hidimar aikin gona, a inda suka yi aikin gona a madinatu Kaulaha tare da Alh. Maidoki, Mahi ƙaya Ƙauranna moda da sauran su, waɗanda su kaɗai ne yara` yan Najeriya waɗanda suka yi karatu a wurin Sayyidi Aliyu Sise, sai Sayyidi Bashir Tijjani Usman, amma shi ba su yi aikin gona tare da shi ba, sai dai sun yi karatu tare da shi a wurin Sayyidi Aliyu Sise.
    Daga cikin abubuwan da suka yi matuƙar farantawa Malam rai, a zaman sa na kaulaha, lokacin an fara aikin gona, akwai wata rana, da wani mutumin mahaifin malam ya zo Madinatu Kaulaha ana cewa da shi malam Yakubu Bichi, sai ya ga malam ya yi shiri ya ci ɗamara zai tafi gona, a lokacin an siya masa keken shanu, don yin aikin gona (da farar safiya misalin ƙarfe shida 6:00am), sai wannan abin ya bawa Malam Yakubu sha’awa, ya yi mamakin irin himmar da ya ga malam ya ɗauka, akan wannan aikin kuma ya ce “in Allah ya yarda in na koma gida sai na shaida wa malam Adamu irin wannan namijin ƙoƙari na ka” kuma ya sa masa albarka lallai harkar ka ta yi kyau, ya tafi, shima malam ya yi tafiyar sa gona, ya cigaba da aiki.
    Bayan malam Yakubu Bichi ya dawo gida bai tsaya a ko’ina ba, sai a wurin Shehu Mal. Adamu (Mahaifin malam), a inda ya shaida masa irin ƙoƙari da hidima da ya ga malam yana yi.
    A wannan lokaci Shehu Malam Adamu yayi matuƙar farin ciki sosai, kuma ya ɗauki takarda ya rubuto wa ɗansa (Imam Muhammad Nasir Adam) wata wasiƙa mai cike da kyawawan kalmomi na sanya albarka da yabo da addu’a a gareshi cikin harshen larafci. Kuma bayan malam ya samu wannan takarda, shima ya yi farin ciki da ganin ta, sannan ya samu gida mai kyau na gilashi irin wanda ake adana hoto ya saka ta a ciki domin muhimmancin ta a wurin sa, kuma ya adana ta tsawon lokaci domin kasancewar ta muhimmin kayan tarihi a wurin sa.

2.7. ABOKANAN MALAM NA KASAR KAULAHA(1960-1968)
1. Mustafa Umaru Gai
2. Baram Sal
3. Keba Bau Kartamba
4. Hadi Jai
5. Kabiru Adam Gyaaranya
6. Mahmudu Ghana
7. Abdullahi Lawan Jega
8. Mustafa (dan sayyida Rukayya Nyass)
9. Magaji dan jada
10.Mahi ƙaya
11.Aminu Bici
12. Abdullahi Gana
13. Haruna Akhi Ankwa
14. Haruna Shalam Ni imal Faida
15. Ali Na Shehu Abdullahi
16. Hussaini Na gidan Shehu Naziru.( Da sauran su).
Haka suka yi ta rayuwa cikin hidimar addini da neman albarkar magabata da malamai, zaman sa a can ya yi sabo da mutane ‘yan Kano da dama waɗanda suke zuwa ba don su zauna ba sai don kai ziyara da neman albarka, haka kuma da yawa daga cikin su suna bada shaida a kan sa cewa jajirtacce ne kuma wayayye ne sannan kuma ya iya mu’amala da jama’a.
Malam ya zauna tsawon shekaru goma sha biyar (15) a garin Madinatu Kaulaha, tun da ya je sau ɗaya ya dawo ya yi shekara ɗaya sannan ya sake komawa. Daga nan kuma bai sake dawo wa ba sai a shekarata 1974, a inda ya dawo gida ya cigaba da sha’anin hidima ga addini da rayuwar al’umma.

3.1. DAWOWAR MALAM GIDA NAJERIYA (1974)
     Malam ya dawo gida Najeriya daga ƙasar Sinigal don ya ci gaba da rayuwar neman ilimi da karantarwa kamar yadda aka ɗora shi a kai, kuma wani babban abin sha’awa shi ne; a ranar da ya dawo gida, ya samu mahaifinsa da mahaifiyarsa da sauran ‘yan uwa da abokan arziƙi baki ɗaya suna lafiya ƙalau cikin farin ciki, kuma baki ɗaya su ka zo suka yi masa barka da zuwa.
     A wannan rana da ya dawo ne mahaifin sa ya ke gaya masa cewa. “Shehu Mal. Mudi Salga (Ɗan Malamina) ya ce in ka dawo yana so ka je a ɗora maka nauyin kula da makarantar da aka kafa ta ƙarƙashin ƙungiyar Munalzamatu Fityanul Islam”, amma da malam ya ji haka sai ya ce “to baba, amma ni nafi so na ci gaba da karatu”, sai Shehu Adamu ya ce “tun da ya riga ya aiko min da wannan buƙatar, ni ba zan iya hanawa ba, domin ɗan malamina ne kuma duk abin da ya nema a wuri na in har ina da shi, to sai na ba shi don haka, sai ka shirya ka tafi”. Wannan ya nuna yadda shehu malam Adamu ya ke ganin girman sheikh Mudi Salga kasacnewar sa dan malamin sa, kuma shi ma Shehu Mal. Mudi Salga yana girmama shehu Mal. Adamu Sabado yadda ya yi la’akari da alaƙar da take tsakanin su da mahaifinsa (Shehu Muhammadu Salga) wadda, alaƙa ce ta biyayya da kyautatawa. Kuma babban abin sha’awa da liman Malam Muhammad NasirAdam ya nuna shi ne; amincewa da yayi da buƙatar da mahaifin sa ya bijiro masa da ita (duk da cewar ta saba da ra’ayin sa). Kuma saboda tsananin biyayya, a ranar da yadawo mahaifn sa ya yi masa wannan bayanin, kuma a ranar ne ya sake ɗaukar jakar sa ya tafi garin Kano wurin Sheikh malam Mudi Salga, don karɓar wannan nauyi da aka ɗora masa. Wannan ma yana ƙara yin nuni da irin ɗabi’ar da malam yake da ita ta biyayya ga magabatan sa da kuma himmar sa, mai matuƙar ban sha’awa, sannan mai wahalar gaske wajen kwaikwayo.
3.2. HADUWAR SA DA MAL. MUDI SALGA DA KASANCEWAR SA A MATSAYIN SHUGABAN MAKARANTAR SABILAL FALAHI
     Bayan malam ya zo, sai Shaikh Mal. Mudi Salga, ya shaida masa cewar “a sakamakon irin jajircewar ka da muka gani da ƙwazon ka da kuma gogewar da kake da ita tun a Madinatu Kaulaha, mun yanke shawarar cewar kai ne za ka riƙe mana wannan sabuwar makarantar Islamiyya da muka kafa”. Kuma hakan ce ta kasance, a inda Malam ya Shugabanci wannan makaranta, kuma ya kawo tsare-tsare masu kyau, waɗanda da dama daga cikin mutane musamman iyayen yara (ɗalibai) suke yabawa da su, kuma kasancewar sa shugaban wannan makaranta, ta sabilal falahi a unguwar Manladan cikin birnin kano a shekarar 1974, a loakci guda kuma yana ware wasu lokuta da ranaku don yin bita ga malaman sa, (yana ba su horo na musamman a kan dabarun koyarwa a zamanance,) kasancewar da yawa daga cikin su, sun yi karatu ne a tsari irin na makarantar Allo, ba Islamiyya ba.Kuma wannan makaranta ta yaye ɗalibai masu yawan gaske. Waɗanda da yawa daga cikin su sun zama malamai waɗansu ma sun zama alƙalai da ma’aikatan gwamnati da kuma ‘yan kasuwa.
KASANCEWAR SA A MATSAYIN SHUGABAN MAKARANTAR FIRAMARE TA NAHDATUL ISLAMIYYA.
    
     Makarantar Nahdatul Islamiyya wadda ita kuma aka kafa ta a shekara ta 1975, a unguwar gwammaja kukar ‘yan caca, wadda marigayi mai martaba sarkin Kano Alh. Ado Bayro ne ya buɗe ta, kuma Marigayi Alh. Sani Mashal shi ne ya gina mata ajujuwa guda tara (9), kuma ita ma aka miƙa ragamar tafiyar da sha’anin karantun ta ga malam, a matsayin shugaban makaranta (Headmaster). A inda yake yiwa malaman makarantar bita a kan yadda ake koyarwa a Islamiyya da kuma dabarun koyarwa a zamanance kasancewar da yawa daga cikin su malaman soro ne, kuma ya cigaba da zama a matsayin shugaban makaranta kuma ana samun ci gaba daki-daki, har aka samu gwamnati ta shigo cikin sha’anin makarantar, ta aiko da malaman gwamnati. Daga cikin malaman gwamnati da malam ya yi musu Head master akwai; Mal. Sani da Khalifa Shaikh Ƙariballah Nasiru Kabara da Mal. Ibrahim Nagoda da Mal. Mudi Nagoda da Barr. Nabahani (na Hisba) da Mal. Lawan Muƙaddas da Mal. Shehu ɗanmarina da kuma Mal. Lawan Abdullahi har shi ma malam ya zama gwamnati ta ɗauke shi a matsayin malami, sannan shugaban makaranta, kamar yadda yake, har zuwa shekara ta 1978, a inda ya tsara yadda za’a kafa makarantar sakandare wadda, idan ɗaliban da suke karatu a firamare sun gama za su ci gaba da karatun su a cikin kuma Allah ya badanasara, aka samu damar kafa wannan makaranta ta gabada firamare (Sakandire) kuma aka ce malam ne zai zama firinsifal amma saboda kasancewar malam bai je makarantar zamani ya samu shahada ba, gwamnati ta ƙi amincewa, da hakan, domin ƙa’ida sai mutum yana da takardar shahada ta gama makaranta sannan za’a iya bashi matsayin firinsifal, kuma duk da cewa, sun amince kuma sun gamsu a kan cewa malam yana da ilimi da ƙwarewa da sanin makamar aiki, matsalar ita ce rashin wannan takardar shahada da bashi da ita. Ganin haka, sai malam ya yanke shawarar komawa makaranta don ya samu katardar shahada wadda za ta ba shi dama, ya zama shugaban makarantar sakandiren da ya kafa don ya samu damar yi mata tsare-tsare ingantattu, kamar yadda ya yi wa makarantar firamaren Nahdatul Islam da kuma makarantar Islamiyya ta Sabilal Falahi.
     Bayan ya yanke wannan shawara sai ya shaida wa Shaikh Malam Mudi Salga, kuma ya amince da wannan hangen nesa da Malam ya yi. Daga nan Malam ya tafi kwalejin horas da malamai ta Katsina, a inda aka nemi alfarmar shugaban makarantar mai suna ``Kinawi`` a kan ya saka malam a cikin ɗaliban da za su ɗauki jarrabawar su ta fita, don malam ya samu damar komawa ya ci gaba da kula da makaratun sa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci,

amma shugaban makaratar bai amince da wannan buƙatar ba saboda kasancewarsa shi shugaban makarantar mutumin Masar ne ba ɗan Najeriya ba ne, yana tsoron ya yi alfarmar da za ta sa ya samu matsala a aikin sa, amma sai ya ce, in malam ya amince zai saka shi a aji biyu, su yi jarrabawar tafiya aji uku da sauran ɗalibai, in an dawo daga hutu ya zama ɗan aji ku (3) sai Malam ya ce ya amince, aka saka shi a aji biyu, (zangon karatu na ƙarshe) kuma ya cigaba da karatun sa har zuwa lokacin da ya kai shekarar ƙarshe, suka ɗauki jarrabawar fita daga makaranta, a inda ya zama shi ne ɗalibi wanda ya fi kowa ƙwazo a wannan shekara, a mafi yawan darussan da suke yi a wannan makaranta, wanda shi ne ɗalibi mafi ƙwazo a darussan Arabic da Hausa da darussan addinin Musulunci da Ilimin koyarwa a aikace da tarbiyya. Kamar yadda wannan takarda mai zuwa take nuna mana;
     Bayan an bashi waɗannan lambobin yabo a matsayin ɗalibi mafi ƙwazo, a wannan shekra, sai wannan ta sa yayi farin jini sosai, har ta kai shugabannin makarantun sakandire biyu suka nemi ya zo makarantar su ya koyar a can, sannan sarkin malamai mai kula da wannan shiyyar ta katsina (chief Education ), shi ma ya nemi da malam ya zo a bashi mota (landroɓer) ya je ya dinga yi wa malamai da limamai bita, sannan zai ɗauke shi aiki a matakin albashi na huɗu (leɓel 04) maimakon matakin albashi na uku kamar yadda ake ɗauka, kuma ya gayawa malam cewar za su yi aiki tare, ba a ƙarƙashin wani daban zai ajiye shi ba, sannan zuwa lokacin da sakamakon jarrabawar su zai fito a sannan kuma, zai mayar da malam matsayin albashi na biyar (leɓel 05). Amma malam bai amince ya karɓa ba saboda burin sa shine ya gama karatun sa ya koma ya ci gaba da kula da makarantun sa a garin Kano.
     Bayan wannan, shima Sharif Abba Abu a lokacin ya gina waɗansu gidaje a katsinan, kuma ya ware guda ɗaya ya ce ya bawa malam ya zo ya zauna a tare da shi a nan garin katsina, nan ma malam ya ce ya amince amma a nemi izinin mahaifin sa, bayan ya yi izini, sai malam ya zauna, a garin Katsina na ɗan wani loakci.

3.3. NASARORIN DA MALAM YA SAMU A GARIN KATSINA A LOKACIN ZAMAN SA NA KARATU A ATC (1978-1981).
     A sakamakon wannan zama da malam ya yi, ya samu damar kafa ƙungiyar Munaz zamatu fityanul Islam reshen Jihar Katsina, amma wannan ƙungiya al’amuran ta basu yi ƙarfi ba, har sai ranar da ƙungiyar Izala ta zo garin katsina ta yi taro, kuma suka kafa lasifika, suka zazzagi manyan waliyyan Allah, irin su Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, da wali ɗan marna da wali ɗan Taku da wali joɗoma da sauran bayin Allah, sannan suka kafirta duk wanda yake ɗariƙa, to daga wannan rana ne malam ya tashi a tsaye ya ƙarawa tafiyar sa ƙaimi, kuma suke fita wa’azi, don faɗakar da al’umma tare da yaƙar wannan gurɓatacciyar aƙida ta zagin waliyyan Allah da kafirta musulmi. Kuma an yi Babbar nasara, wanda a sakamakon haka ne ƙungiyar Munaz zamatu fityanul islam ta yi ƙarfi a Jihar Katsina, kuma har a ka samu damar gabatar da Babban taron ta na ƙasa gaba ɗaya a Jihar katsina. Bugu da ƙari a zaman sa na Katsina a wannan lokaci ya samu damar kafa makaranta a gidan sharif Abba Abu mai suna ``Sabilul Falahi mai ajujuwa guda tara (9) da ɗalibai da dama.
3.4. ABOKAN MALAM NA KATSINA
1. Audu Data Masanawa
2. Malam Salisu K/’Yanɗaka
3. Abbati K/’Yanɗaka
4. Shehul Hadi Ja afar
5. Balan M. khamisu Yarinci
6. Dan almajiri M. khamisu
7. Saraja M. miko (cikin gida)
8. Ummeme K/Yan ɗaka
     Bayan wannan gwagwarmaya da malam ya sha fama, zuwa wani lokaci sai ya miƙa sha’anin tafiyar da ƙungiyar fitiyanu a hannun ‘yan’uwa abokan gwagwarmaya, kuma ya yi sallama da su da niyyar zai komagarin Kano don ya ci gaba da kula da makarantun sa, duk da cewar da farko Sharif Abba Abu da sauran jama’a ba su yarda ya tafi ba, amma daga baya su ka haƙura suka ƙyale shi, kasancewar Shaikh Mal. Mudi salga ya nuna damuwar sa a kan lallai sai Malam ya koma garin kano, saboda makarantun da ya tafi ya bari, suna buƙatar kulawa, (domin abubuwa sun fara ja baya dangane da sha’anin ci gaban waɗannan makarantu). Bayan malam ya koma garin kano ya je ya tarar da makaranta a cikin yanayi na koma baya matuƙa, kuma hakan ya sa sai da malam ya ɗauki tsawon wata goma sha biyu (12) yana gyara kuma a cikin wannan watanni goma sha biyu (12) kullum karfe shida da rabi na safiya yake barin gida, ya koma karfe shida na yamma, sannan ƙarfe bakwai na safiya a ofishi take yi masa, ba Alhamis ba Juma a, har sai da ya samu nasarar gyara wannan makaranta kuma aka cigaba da gudanar da karatuttuka kamar yadda ake yi a da.
     Bayan wannan kuma, in za’a iya tinawa a baya cewar malam ya koma karatu ne don ya samu takardar shahada. Wadda za ta bashi dama ya riƙe makarantar sakandiren da ya kafa, a matsayin shugaban makaranta.Kuma a sanadiyyar wannan taifiya da ya yi, ya zama ita ma ɓangaren sakandiren wadda ya saka mata suna; Shaikh Tijjani Usman zangon bare-bari shi ma karatun ya ja baya matuƙa, sai Shaikh Mal. Mudi Salga ya nemi Mal. Da ya ɗauki matakin da ya dace don ganin wannan makaranta ta farfaɗo, kuma ya sake yin tsare-tsare don kwarjinin makarantar ya dawo, ya fi na da.
     Bayan malam ya yi duk tsare-tsaren da suka kamata sai ya jajirce ba dare ba rana har Allah ya sa makaranta ta farfaɗo, kuma hukuma ta aiko musu da shugaban makaranta (Frinsifal). Wadda a wannan lokaci aka turo Malam Musa Baƙin Ruwa, wanda shine shugaban makarantar na farko da hukuma wamnati ta turo musu, a inda shi kuma malam ya kasance mataimakinsa, kuma bugu da ƙari shugaban ɓanagren firamare, (Safe da yamma ) duk da cewa a lokuta da dama ba ya zama da yamma, sai dai mataimakin sa Mal. Muhammadu ɗan Marina, wanda shine wanda yake taimaka masa, kuma yake kula da ɓangaren yamma, kuma abubuwa suna tafiya cikin tsari da taimakon ubangiji.
    

3.4. HAƊUWAR MALAM DA KHALIFA SHAIKH ISHAKA RABI’U
Duba da yadda Malam yake da himma da kwazo ta sa Khalifa Mal. Ishaƙa Rabi`u idan wadansu al`amura sun taso yakan aika mutane daga ofishin sa yace‘‘kuje ku samu Mal. Nasiru a gwammaja ‘‘ a wasu lokutan ma har yakan aika a kirawo masa shi, ana haka har yau da gobe har ta kai Halifa ya jawo shi a jiki sosai, kuma alokacin da aka kammala ginin gidajen da Halifa ya gina su don Liman da Na‘ibin masallacin Goron Dutse, lokacin Malam yana a Matsayin Na‘ibi, sai Halifa ya ce ya koma Goron dutse gidan Na‘ibin masallaci ya zauna. Bayan ya tare a gidan sai yayi la‘akari da yadda unguwa take cika kuma ga ajujuwa amma ba‘a karatu yadda ya kamata , sai ya shawarci khalifa Mal. Ishaƙa Rabi‘u akan cewar ya kamata a samar da Makaranta wadda ‘ya‘yan unguwa za su dinga karatu a ciki, kuma Halifa ya amince da wannan shawara sannan ya dora masa alhakin tsara yadda makaranta za ta kasance. Kafin Malam ya kai ga kammala wannan aiki sai Halifa yayi wata tafiya mai nisa wadda har sai bayan an kammala ginin makarantar wadda ya saka mata sunan mahaifin Halifa (Shaikh Muhammadu Rabi‘u Islamiyya)
kuma har an soma karatu a ciki sanna ya dawo ya tarar al‘amuran Makaranta sun kankama sannan ya tarar an tsara komai yadda ya kamata, wannan ya faranta wa Halifa rai sosai, sai dai kudin da aka saka na makaranta ne ya yi kadan ba zai rike makarantar ba, anan ne kawai yayi gyara yace a mayar da shi yadda makaranta za ta samu ta tsaya da kafar ta saboda gaba. Sai shi ma Malam yace ‘‘Nima na yi la‘akari da haka amma gudun kada mutane su ce na bude makaranta ina neman kudi shine dalilin da ya sa na bar shi a haka amma za‘a gyara‘‘. Wannan makaranta ana yin karatu da safe a matsayin firamare sannan da rana a shiga islamiyya haka nan da daddare akwai ta matan aure, wadda suma aka bude musu. Daga baya kuma aka sake bude bangaren sakandare wadda daga wancan lokaci zuwa yanzu ta yaye dalibai da dama kuma daga cikin su akwai mahaddata masu tarin yawa da kuma wadansu da suka yi fice a wasu bangarori


3.5. NADA SHAIKH MALAM ISHAƘA RABI`U A MATSAYIN KHALIFAN TIJJANIYYA NA NAJERIYA.
     Bayan rasuwar Khalifa Sir, Muhammadu Sunusi (Murabus),sai ya kasance babu wani wanda aka dora wa wannan nauyi na khalifanci a Najeriya.
     Wata rana da daddare Shaik Mal. Ishaƙa Rabi‘ù yana zaune a gida ya gama shirin yin bulaguro zuwa kasar turai idan gari ya waye, sai ya ji kiran waya, bayan ya dauka sai ya ji muryar Sharif Ibn Saleh daga moroko wanda ya kasance jika ne ga Shaikh Ahmadu Tijjani (RA), tsakanin sa da Shehu Tijjani mutum hudu ne, kuma shine khalifan sa a wancan lokaci. Bayan sun gaisa sai yace‘‘ Mal.Ishaƙa ina neman ka ‘‘ sai Mal. Ishaƙa yace ‘‘Sharif na shirya gobe zan yi tafiya ta ta kasuwanci, amma in Sharif ya ce na fasa na zo, to shi kenan, sai Sharif ya ce ‘‘ To nayi ma izini ka tafi amma ina so ka turo min wani amintaccen ka,‘‘bayan sun kammala sai ya kira Mal. Muhammad Nasir Adam a waya yace yana son ganin sa. Bayan ya zo sai ya shaida masa yadda suka yi da Sharif Ibn Saleh, kuma ya wakilta shi a matsayin amintaccen sa ya tura shi Moroko wurin Sharif kuma ya bashi sakon hadiyya zuwa wajen Shaikh Abdullahi Nyass dan maulan mu Shehu Ibrahim (Kaulaha).
     Bayan ya je kaulaha ya isar da sakon Mal. Ishaka Rabi‘u sai ya wuce Moroko wurin Sharif, amma kasancewar ya isa Moroko cikin dare sai Allah ya hada shi da wani muridin Sharif wanda ya kwana a wurin sa, da gari ya waye sai suka tafi kofar gidan Sharif aka yiwa Malam iso, aka zo daga cikin gida aka karbi jakar sa, aka shigar dashi wurin Sharif, suka gaisa ya tambaye shi labarin mutanen Kano, da sarki da Mal. Ishaƙa da sauran su. Bayan sun gama gaisa wa sai yake tambayar sa yana cewa ‘‘Wai Nasiru tun bayan rasuwar Khalifa Sunusi wa aka nada a matsayin Khalifan Tijjaniyya a Najeriya’’? sai Malam yace ‘‘Ai har yanzu babu wanda aka nada’’ sai Sharif yace to ai hakan ba daidai bane, yaya jama‘a mai tarin yawa haka za‘a bar ta babu jagora’’, ya cigaba da cewa ‘‘To Nasiru zan nada Jagora,na san wanda zan nada, Malam Ishaƙa zan nada na san soyayyar sa da mu, kuma sama da Shekara Arba‘in (40), ya yi yana yi mana hidima, shi zan nada, Nasiru zaka ga abin mamaki, Allah ya sa Najeriya a tafin hannu na a yanzu abin da nake so kawai shi Allah zai yi a Najeriya’’, a lokacin da Sharif yake wannan jawabin ya nuna matukar damuwa, da nuna muhimmanci ga abin da yake fada sosai, har malam yake mamakin yanayin da Sharif ya shiga. Daga karshe Sharif yayi addu‘a suka shafa, yace da Malam ‘‘zan sake kiran ka‘‘ aka kai Malam masaukin sa, bayan kwana daya sai ya sake kiran Malam ya yace da shi ‘‘Malam Nasiru akan maganar da muka yi da kai, na yanke shawara zan shaida wa sahabban Shehu Tijjani kuma zan shaida wa ‘ya‘ya na, sannan zan baka takarda ka tafi da ita. Da gari yaw aye Malam ya karbi takarda daga hannun Sharif suka yi sallama ya taho da ita ya dawo Sinigal (kaulaha) suka yi sallama da Shaikh Abdullahi Nyass ya taho Najeriya amma bai shaida masa yadda suka yi da Sharif ba.
     Bayan ya dawo Kano sai ya isar da takardar nadin Khalifanci ga Shaikh Malam Ishaƙa Rabi‘u, ganin haka sai Malam Ishaƙa Rabi‘u ya sanar da manyan malamai (Jagorori) na darikar Tijjaniyya na Najeriya, bayan sun zauna a tsakanin su sun yi shawara sai suka ce ‘‘Mu ‘yan Tijjaniyya ne amma ta hannun Shehu Ibrahim muka shiga don haka, duk abin da za‘a yi na Shehu Tijjani sai idan ‘ya‘yan Shehu Ibrahim sun amince, don haka a tura Kaulaha a shaida musu, a nan ma sai aka ce wa za‘a tura? Su da kansu suka ce ‘‘Ga Mal. Nasiru a tura shi ‘‘ Bayan ya je sai ya gatarwa Shehu Abdullahi Nyass takarda da Sharif Ibn Saleh ya bayar ta nadin Mal. Ishaƙa Rabi‘u a matsayin Khalifan Tijjaniyya na Njeriya, da kuma abin da manyan jagororin darikar suka ce, sai Shehu Abdullahi ya karbi takardar ya bude yace ‘‘Nasiru shin da ka zo ka kwana a nan wannan takardar ba ta tare da kai ne‘‘? sai yace ‘‘Akaramakumullah tana hannu na‘‘sai Shaikh Abdullahi ya kara tambayar sa yace ‘‘to ya ba ka nuna min ba?‘‘ sai yace ‘‘ai ba‘a ce in nuna muku ba, ina gudun kada naje na yi ba dai dai ba,‘‘ sai ya ce ‘‘gaskiyane ai wasa nake yi maka Nasiru, ni na fi kowa murna da wannan takardar, ya ci gaba da gaya masa cewar ‘‘Nasiru yau Shekara ta uku (3) ina rokon Allah ya fito mana da wanda zai iya jagoranci harkar almajiran Shehu a Najeriya, yau ni Allah ya biya wa bukata, ka je ka koma masaukin ka zan samu sahabban Shehu mu yi maganar, kuma zan samu ‘ya‘yan Shehu mu tattauna abin da muka yi zan baka takarda ka tafi da ita. Da gari ya waye sai Shehu Abdullahi ya sa aka kira Malam ya bashi takardar amincewa da Shaikh Malam Ishaƙa Rabi‘u kamar yadda suka yi shawara, kuma bakin su ya zo daya akan haka, sannan ya daga hannu ya yi wa Mal. Nasiru addu‘a suka shafa, yace masa Allah ya kiyaye Allah ya kai ka lafiya.
     Daga wannan rana da Malam Muhammad Nasiru Adam ya zo da wannan takarda daga wurin Shehu Abdullahi Nyass, sai wadannan jagorori na darikar Tijjaniyya suka gamsu tare da amincewa da Khalifacin Malam Ishaƙa Rabi‘u a Najeriya.
     A shekara ta 1983-1984, Khalifa Shaikh Mal. Ishaƙa Rabi’u ya gina masallaci, wanda shine masallacin Juma’a na farko na ‘yan tijjaniyya a Kano. Wannan masallaci an gina shi ne a shekara ta 1983 ganin haka, sai malam ya shaidawa Shiakh Mal. Mudi salga cewar idan an buɗe wannan masallaci yana so zai bada ta sa gudummawar ta kiran sallah, (wato ya na so ya zama ladanin wannan masallaci), kuma Mal. Mudi salga ya yi farin ciki da jin wannan muhimmiyar gudunmmawa da Malam zai bayar kuma yaje ya sami Khalifa Mal. Ishaƙa Rabi’u ya shaida masa cewar an samu wanda zai dinga kiran sallah a masallacin, kuma shima Khalifa ya amince da hakan, sannan ya ce a turo masa wannan mai kiran sallar don su gana, bayan malam ya je ya sami Khalifa Sheikh Ishaƙa Rabi’u a (Inyass House) wanda yake a unguwar ‘Yankaba, bayan sun gana zuwa lokacin sallar isha’ i sai malam ya tashi ya kira sallah, bayan an idar sai Khalifa Sheikh Ishaƙa Rabi’u ya yaba masa ya ƙarfafa masa gwiwa har ya yi masa laƙabi da “Muwazzinu” wanda an ɗauki lokaci mai nisa Halifa yana kiran malam da wannan suna.
     Bayan an buɗe masallaci an fara yin sallah a ciki, sai mutane suka fara ganin tsare-tsare irin wanda ba’a saba ganin ladanai suna yin irin su a masallatai ba, a inda ya kasance yana kunna karatun alƙur’ani da Asuba, da kafin sallar Azahar, da La`asar,haka yana sa muryar makaranta daban daban kamar su Shaikh Abdulbasiɗ, Muhammad Khalilul husari, da dai sauran su wanda wannan yana daga cikin abubuwan da mutane suke jin daɗin sa, sannan ranar Juma’a yana yin wa’azi a masallaci kafin liman Mal.Ashiru ya shigo don fara gabatar da huɗuba, wannan wa`azi ya ƙarawa masallacin daraja da jama`a saboda wa`azin yana da jan hankali sosai, har ta kai mutane da yawa suna zuwa masallacin da wuri ranar Juma’a don su ji wannan wa’azi wanda a sakamakon wannan wa’azi da waɗannan tsare-tsare sababbi da ya kawo su wannan masallaci, sai Khalifa Mal. Isahaƙa Rabi’u yake mamakin lamarin wannan ladani, kuma yake jin daɗin waɗannan tsare-tsare da yake yi, har ta kai yana aikawa a kirawo masa shi don neman shawara har a wani lokaci liman Mal. Ashiru ya ke gaya wa Khalifa cewar, “wannan yaron lallai a ƙara riƙe shi, domin na lura duk abin da ake so in aka saka shi a gaba ba za’a ji kunya ba”, kuma shi ma Halifa ya yi la’akari da hakan domin duk abin da aka nemi shawarar sa, in ya bayar ana samun nasara da natija.

3.4. KASANCEWAR MALAM A MATSAYIN SAKATAREN CIBIYAR ADDININ MUSULUNCI TA SHAIKH MUHAMMADU RABI`U
A sakamakon waɗannan dalilai da muka yi bayanin su a sama, Khalifa malam Ishaƙa Rabi’u ya soma saka malam Muhammad Nasiru a cikin sha’anin sa musamman wanda ya shafi harkar addini da sha’anin cibiyar addinin musulunci ta Sheikh Muhammadu Rabiu wadda wadda khalifa ya assasa ta kuma take gudanar da al’amura don taimakon addinin musulunci da yaɗa shi, sannan tana da alaƙoƙi masu yawa tsakanin ta da sauran ƙasashen duniya musamman na larabawa da sauran ƙasashen Afrika, wanda duk inda ake buƙatar wakilci, sai Khalifa ya tura Malam Kuma duk inda aka tura shi ba’a jin kunya, a matsayin sa na wanda Khalifa Sheikh Mal. Ishaƙa Rabi’u ya naɗa sakataren wannan gidauniya mai albarka an yi masa wannan naɗi a shekara ta 1984. 3.5. KASANCEWAR SA A MATSAYIN NA‘IBIN MASALLACIN JUMA’A NA SHAIK MUHAMMADU RABI U G/DUTSE KANO.
     1. Malam yana riƙe da wannan nauyi, na waɗancan Makarantu kuma in ba’a manta ba shine ladanin masallacin Shaikh Muhammadu Rabi’u (Goron Dutse), sai aka samu wani yanayi wanda wannan masallaci ya zama babu na’ibi, kuma manyan shugabanni suka zauna suka yanke shawara a kan cewar Malam Muhammad Nasir za’a bawa matsayin Na’ibin wannan masallaci, amma sai Khalifa Malam IshaƙaRabi’u ya shaida musu cewar, “idan aka gaya masa za’a naɗa shi ba zai yarda ba, don na san shi da tawalu’u, sai dai a gayawa Shaikh Abdullahi Inyass ya yi masa izini ya Kawo kansa a naɗa shi”. Kuma haka aka yi, Shehu Abdullahi (Ɗan Shehu Ibrahim) ya naɗa shi, aka yi taro har malam yake karanta jawabi cikin harshen larafci, na godiya a gaban manyan shugabannin ɗariƙar Tijjaniyya, amma a wannan lokaci muryar sa tana rawa saboda an girmama shi, da abin da yake faɗa cewa ko a mafarki bai taɓa tunanin zai zama limamin Hamsus salawati ba, amma yau ga shi a matsayin Na’ibin masallacin Juma’a, lallai wannan abu ya sa shi ya ji nauyi matuƙa da gaske, Jama’a da dama sunyi farin ciki Malam ya zauna tare da liman Malam Ashiru wanda shine Limamin wannan masallaci, wanda har wata rana malam yake cewa da malam ashiru “ina sha’awar yadda kake canja huɗubar sallar Juma’a, ina ganin ya kamata a samu a dinga adana su a wani kundi don amfanuwar al’umma”. Wanda a lokacin da yake gaya wa malam Ashiru wannan maganar bai san cewar shima zai zama limami ba, wanda a loakcin liman Mal. Ashiru yake bashi amsa cewar; ba dan yanayi ba, da duk juma’a sai na sake sabuwar huɗuba. Wanda a wannan lokaci shehu Mal. Ashiru yana da huɗubobi a ƙalla guda bakwai (7), wanda idan aka yi la’akari da zamani, zamu iya cewa malam Ashiru ya yi ƙoƙari, domin mafi akasarin masallatai huɗubar su guda ɗaya ce ko biyu, in ta yi yawa uku (3).
     Suna nan tare da liman Mal. Ashiru cikin kyakkyawar fahimtar juna da kuma biyayya da Malam yake yi masa, har zuwa lokacin da ƙaramar hukuma ta yanka musu alawus a matsayin su na limamai wanda a lokacin da aka fara kawowa, sai aka bawa Mal. Ashiru da nasa da na malam, bayan malam Ashiru ya kira malam da niyyar zai danƙa masa alawus ɗin sa, sai ya cewa malam ashiru “ka riƙe kaso na gaba ɗaya, in yaso ni ayi min addu’a.”
     Wannan abu ya bawa liman Mal. Ashiru mamaki, kuma ya ji daɗi sannan ya yiwa malam addu’a kamar yadda ya nema da wani watan ya zo sai aka sake aiko wa da mal. Ashiru alawus ɗin su (na sa da na malam), kuma ya nemi malam da niyyar zai bashi, wannan kuɗi, sai malam ya sake cewa a yi masa addu’a kuma a wannan lokaci ma bai karɓi kuɗin ba, haka aka dinga yi duk wata idan an kawo kuɗin alawus, sai liman Mal. Ashiru ya shaida wa malam cewa, an kawo kuɗi shi kuma malam sai ya ce “to a yi min abar” (yana nufin a yi masa addu’a a madadin kuɗin) haka suka dinga yi har zuwa loakcin da shima malam ya zama limamin Juma’a na masallacin Shaikh Ahmadu Tijjani, wanda kafin haka, sai da liman Mal. Ashiru ya taka rawa wajen nunawa al’umma cewar Mal. Muhammad Nasir Adam mutum ne mai ilimi. Saboda a lokacin da liman Mal. Ashiru ya yi tafiya, na wasu ‘yan satuttuka, sai da malam ya samu damar rubuta huɗubobi a ƙalla guda uku, waɗanda ya gabatar da su a kan mumbarin juma’a kuma bayan liman Mal. Ashiru ya dawo daga wannan tafiya, na ɗan-wani-lokaci, sai ya sake yin tafiya zuwa aikin hajji,wanda ya je ya daɗe, sosai a can, a inda shi kuma malam ya nuna baiwar da Allah ya yi masa da himma sai da ya shirya huɗubobi a ƙalla guda bakwai(7), wanda wannan abu ne abin a yaba masa matuƙa da gaske, har zuwa lokacin da liman Mal. Ashiru ya dawo daga aikin Hajji kuma ya samu masallaci, komai yana tafiya yadda ya kamata. Sannan duk da cewar liman Mal. Ashiru ya dawo, ya kamata ya cigaba da jan sallah, amma bai yi hakan ba, sai ya cewa malam ya cigaba da jan sallah, a inda liman Mal. Ashiru dashi da Khalifa Shaikh Ishaƙa Rabi’u da Mal. Salisu Ɗanruwantsa suna baya suna bin sa wanda haka ya zama kamar wata jarrabwa ce ake yi masa, kuma a shekarar ne aka kammala ginin masallacin juma’a na Shaikh Ahmadu Tijjani, dake Ƙofar Mata kuma aka yanke shawara cewar Liman Muhammad Nasir Adam shi ne ya kamata ya zama limamin wannan masallaci.

KASANCEWAR SA A MATSAYIN LIMAMIN MASALLACIN JUMA’A NA SHAIKH AHMADU TIJJANI (R.A) (K/ MATA, KANO).
     Kasancewar Malam a wannan matsayi zabi ne na Allah da kuma cancanta, amma duk da haka sai da wasu suka kawo suka, akan haka, suna ganin cewar shi ba mahaddaci bane, amma sai Liman Mal. Ashiru ya mayar musu da amsa cewar “Ai mumbarin Juma’a ba tilawar Alƙur`ani ake yi a kai ba, ilimi ake buƙata”. Kuma aka yanke shawarar an bawa liman Muhammad Nasir Adam limancin wannan masallaci, a wata ranar juma’a bayan an idar da sallar juma’a wadda malam ya gabatar, sai Khalifa Shaikh Ishaƙa Rabiu ya sanar da jama’a cewar “Limamin da ya yi mana sallah yau, shine wanda in Allah ya kaimu sati mai zuwa zai ja mu sallah a sabon masallacin Juma’a na Shaikh Ahamdu Tijjani K/Mata a matsayin Babban limamin masallacin, kuma aka yi addu’a jama’a suka yi farin ciki matuƙa har zuwa lokacin da sati ya kewayo, wanda a baya idan ba’a manta ba na shaida mana cewar malam yana da huɗubobi waɗanda ya shirya su lokacin yana Na’ibi lokacin da liman malam Ashiru ya yi tafiya kuma waɗannan huɗubobi aƙallah za su kai guda bakwai (7) malam ya tattara su a cikin wani littafi ya adana su, amma wani abin mamaki shi ne yadda malam ya nemi wannan littafi ya rasa shi, duk inda yake tinanin ya saka wannan littafi sai da ya duba shi amma bai gan shi ba, sai ya yi addui’a ya ce Allah ya sa haka shi ne ya fi alheri, sannan ya ce: “Zan buɗe wannan masallaci da huɗubar Shehu Ibrahim Nyass don neman albarka, amma ya Allah ina roƙon ka ka amince min a bisa alƙawarin da na ɗauka da yardar ka, daga wannan Juma’ar har zuwa nan da shekara guda ba zan maimaita huɗuba ba sai shekara ta kewayo da yardar ka.” haka kuwa aka yi a inda malam ya buɗe masallaci da ɗaya daga cikin huɗubobin Maulan mu Shaikh Ibrahim Nyass, kuma tun daga wannan juma’ar malam ya fara shirya huɗubobin sa a kowacce juma’a ba tare da ya maimaita ba har tsawon shekara guda Cur, ya na yi yana adana su har sai da ya gama, sannan ya mayar da su littafi guda, wanda yake ɗauke da waɗannan huɗubobi da ya gabatar a tsawon wannan shekara guda da ya yi yana jan sallah a wannan masallaci sannan ya haɗa su tare da huɗubar ɗaurin aure da ta raɗin suna, a in da ya saka wa wannan littafi suna: “Almufidu Lilkhuɗaba’i wal Murshidin”. Kuma Khalifa shaikh Ishaƙa Rabi`u ya ɗauki nauyin saka wanna huɗuba a gidan talabijin na NTA duk sati har tsawon Shekara ɗaya da wata shida, Wanda wannan littafi na Malam mai dauke da huɗubobi ya samu karɓuwa matuƙa, kuma an sabunta bugun sa har sau biyar a tsawon shekaru ashirin da ‘yan kai, tun daga lokacin da aka yi bugu na farko zuwa yau, sannan alumma sun amfana da wannan littafi, wanda malam ya samu damar yaɗa shi a wurare da dama a ƙasar nan, har ma da ƙasashen waje, wanda daga cikin muhimman gurare da malam ya samu damar kai wannan littafi har da laburare na masallacin Annabi Muhammadu (SAW) da ke madina. kamar yadda wannan hoto mai zuwa yake nuna mana malam a kofar dakin karatu wannan masallaci lokacin da ya kai kwafin Littafin don amfanin masu nazari na duniya baki daya:
     Fatan mu shi ne Allah ya kara wa malam haske da budi don ya samu damar cigaba da wannan hidima da yake yiwa addinin musulunci.
     Wani abin sha`awa shine yadda wasu da dama daga cikin bayin Allah suka samu damar buga wannan littafi tare da yaɗa shi a cikin al`umma, waɗannan mutane gasu kamar haka;
1-Hon. Speaker Aminu Waziri Tambuwal
2-Mal. Ibrahim Shekarau
3-Hon. Kawu Sumaila
4-Marubucin Littafin (da kansa)
5-Jam`iyyatudda`awa (Libiya) ta buga shi kuma ta yaɗa shi a yankin ƙasashen Asiya sannan ta saka shi a Internet (yanar gizo).
6-Sannan akwai wani bawan Allah (Mal. Hadi Dutsamma) yayi rubutu akan wanna littafi kuma ya samu shaidar Majistera, sannan yana shirin ƙara yin rubutu akai don samun digiri na uku (PHD).

ZAMAN DA MALAM YAYI A UNGUWAR MAGOGA DA SANKA KAFIN TAFIYAR SA KAULAHA DA BAYAN YA DAWO
     Malam yayi zama a unguwar Magoga cikin birnin Kano don neman ilimi, ya yi karatu a wajen Malam Abdulmajidi Jibril. Abinda ya karanta a lokacin shi ne ``Risala`` da sauran littattafai masu binta irin su ishiriniya, ibn Rushud da dai sauran su. Mai ja musu baki a lokacin shi ne Malam Umaru matazu, kuma abokanan karatun sa a wancan lokaci su ne; Malam Mahi, malam Abdullahi Nadankali da Alh. Gambo na Alh. Inuwa karaye, Malam Muhammadu Zariya, Malam Mal. Ummaru matazu yana jan karatu daga ƙawa`idi zuwa Risala, daga nan sai su malam su tashi sai manyan almajirai su zauna, Mal. Salihu Argungu sai ya kama jan Askari zuwa sama, Malam yana yin bita wajen mai sunan Malam, Mal. Abdullahi Bindawa da Mal. Hamza Kankara, abokan karatun sa a wajen maisunan malam su ne; Hamza da siraja da dai sauran su.
     Bayan malam ya dawo daga kaulaha 1974 kafin aikin ya kankama na jagorancin makarantu, ya kasance da rana ya na zuwa wajen Mal. Abdulmajidi yana yin karatun Mukhtasar Khalil a cikin masallacin shehu mal. Salga da ke unguwar magoga birnin kano. Sannan da safe yana zuwa daukar karatu gida Shehu Mal. Atiku sanka wajen Mal. Bukhari Kamba yana karatun Alfiyya ta ibn malik da Nahwu da mukamatul Hariri. Abokanan karatun sa sun hada da : Mal. Nasiru ƙauran Namoda da Mal. Muhammadu Dan Katsina da Mal. Yahaya na Malam Hussaini da dai sauran su. Sannan da la`asar Malam ya na zuwa wajen Maisunan malam ya karanta Alfiyatu ɗariƙ da badarunnada da Albalagatul wadiha da kuma bitar mukhtasar Khalil wanda yake koyo daga wajen Malam Abdulmajidi, maija masu baki shi ne malam Hussaini gaskiya tafi karatu. Abokan karatun sa alokacin sun haɗa da: Salihu Argungu, Mal. Jakara, Sama`ila Gamdare, Alh. Musa kalla, Mal. Lawan gajere, Mal. Lawan Dogo da dai sauran su.
     Makarantar Mal. Abdulmajidi cike take da almajirai daga garuruwa daban-daban kamar; Katsina, Batsari, Kurfi, Rimi, Nijar, Kamaru, da sauran su.

4.1. GUDUMMAWAR MALAM GA ADDININ MUSULUNCI DA SAURAN AL’AMURAN RAYUWA
     Kamar yadda muka karanta a babi na ɗaya da na biyu cewa Malam ya taso a gida wanda ake bawa addini gudummawa ta fuskar karantarwa da tarbiyyantarwa, kuma munga ilimi da kyawawan dabi’u daga mahaifinsa da `mahaifiyarsa, sannan kuma malaman sa waɗanda su ma sun taka gagarimar rawa wajen gina masa kyakkyawan tsarin rayuwa da saita shi ta yadda zai amfani kansa kuma har waɗansu su amfana da shi, kuma kamar yadda muka sani duk abin da Ɗan-Adam yayi don cigaban kansa, to ya ba wa kan sa gudummawa ne, haka duk abinda ya yi don cigaban wani to ya bashi gudummawa ne. Amma larabawa suna cewa mara abu baya bada shi, don haka duk wanda aka ce ya kai matsayin ya bada gudummawa to akwai abin da Allah ya hore masa na baiwa wanda za’a amfana.
     Don haka zamu iya cewa Malam ya samu damar bawa kansa da sauran al’umma daban-daban gudummawa a fannin da Allah ya yi masa baiwa, wannan fanni shine; ilimin addini, shi kuma ilimin addini ga duk wanda ya sa same shi, ya samu wani babban al`amari da zai yi amfani da shi wajen bada gudummawa mai faɗi, a ɓangarori daban-daban, kuma kaɗan daga cikin ɓangarorin da Malam ya bayar da gudummawa sun haɗar da:
4.1.1. GUDUMMAWAR SA A CIKIN SHA’ANIN ƘUNGIYOYIN ADDINI
     i. Ƙungiyar Mataimaka Masallacin shehu Ibrahim Inyass dake madinatu Kaulaha (Jam`iyyatu Ansaril masjidi):
     Wannan Kungiya Malam ya kasance wakili a cikin ta, kuma ya riƙe matsayin sakatare na wannan ƙungiya a inda suke bawa masallacin Maulanmu Shehu Ibrahim Inyas gudummawa ta tsaftace shi da kuma aikin tattara kuɗaɗe don yin hidima ga masallaci a shekara ta 1967. Babban abin sha’awa ga wannan ƙungiya shine kasancewar waɗanda suka kafa ta hausawa ne mazauna garin Madinatu kaulaha waɗanda suke karatu a can, kuma suka yi kishin abin da ake yi na taimakawa addinin musulunci, a sanadiyyar haka ne suka samar da wannan ƙungiya, wacca bayanin tsarin shugabancin ta ya gabata a babi na biyu.
     ii. Ƙungiyar Ɗaliban Makarantar Sayyadi Aliyu Sisa da ke Madinatu Kaulaha:
     Wannan ƙungiya mai suna ``Jam`iyyatu ɗullab li’ilƙa`il khiɗab Almu assasa fi dari sayyidi Aliyu sise`` a shekara ta 1969-1973, ɗaliban gidan Sayyidi Aliyu Sisa ne suka kafa ta a junan su, kuma dalilin kafa wannan ƙungiya shine, domin su bawa kansu wani horo wanda zai ba su damar iyawa tare da tsara huduba ingantacciya, mai ma’ana a cikin harshen larafci, a inda suke taruwa gaba ɗayan su, kowa yana tashi yana gabatar da tasa huɗubar mai ma’ana a cikin harshen larafci, duk inda aka ji kuskure, sai a yiwa Mutum gyara, a sakamakon haka wadannan dalibai a ciki har da Malam, sun samu gogewa wajen iya gabatar da huɗuba da neman ƙwarewa wajen Magana da larafci da jawabi a gaban mutane, sannan sun fita daban a cikin sauran ɗalibai, sannan sun yi fice an san su a garuruwa daban daban, wanda Malam ya kasance misali daga cikin su.
     iii. Ƙungiyar Munazamatu Fitiyanul Islam a garin kano Najeriya:
     Wannan ƙungiya wadda take karkashin jagoran Shaikh Mal. Mudi Salga, an kafa ta ne ƙarƙashin ɗariƙar Tijjaniyya don taimakawa harkokin addinin musulunci, a Najeriya wadda Maulan mu Shehu Ibrahim Nyass shine wanda ya ƙarfafi kafa ta, kuma ta bada gagarumar gudummawa wajen ilimantar da al’umma da wayar musu da kai, a inda suka ɗora wa Malam nauyin kula da Makarantun da aka kafa ƙarƙashin ƙungiyar wanda zamu iya cewa daga cikin manya manyan nasarorin da wannan ƙungiya take alfahari da su har da wadannan Makarantu waɗanda bayanan su da gwagwarmayar da Malam ya yi wajen tabbatuwar nasarar su ya gabata a babi na uku kuma suna ɗaya daga cikin tarihin gudummawa ababen alfahari da Malam ya bawa addinin musulunci, wadda muke fatan Allah ya karɓa daga gare su, muma ya haɗa mu a cikin ladan, kuma ya riƙe muƙamin sakataren hukumar ilimi na ƙasa baki ɗaya a wannan ƙungiya. 1978- 1989.
     iv. Kafa Reshen Ƙungiyar Munalzamatu Fitiyanul Islam a Jihar Katsina:
     Mun ji a cikin babi na uku cewar Malam ya koma karatu na zamani don ya samu Shahadar da zata bashi damar cigaba da kula da Makarantar sakandaren da ya kafa a matsayin shugaban makaranta ko mataimaki, a inda ya zauna a Jihar katsina daga shekara ta 1979 zuwa shekarar 1981 wanda hakan ya ba shi dama ya kafa reshen ƙungiyar Fitiyanu a Jihar Katsina wadda har zuwa wannan lokaci wannan kungiya tana nan, kuma tana cigaba da gabatar da ayyukan ta kamar yadda ya kamata, kuma kadan daga cikin nasarorin wannan kungiya sun haɗa da haɗa babban taron ƙungiyar na ƙasa wanda aka gabatar a Jihar Katsina, da kuma kafa Makarantun Islamiyya da gabatar da wa’azi a wurare da dama da dai sauransu.
     v. Ƙungiyar Limaman Jihar Kano:
     Malam ya kasance ɗaya daga cikin wakilan Ƙungiyar limaman Jihar Kano, a inda aka naɗashi muƙamin mataimakin Shugaban ƙungiyar a shekara ta 2000, kuma gabaki dayan wakilan ta limamai ne na Jihar Kano, amfanin kafa ta shine samar da haɗin kai da fahimtar juna tsakanin limamai da kuma samar da kyakkyawan tsarin rayuwa ga al’ummar musulmi ta hanyar shirya huɗubobi masu ma’ana da kawo hadin kai da zaman lafiya da walwalar al’ummar Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.
     vi. Ƙungiyar Limaman Arewa:
     Banda ƙungiyar limaman Jihar Kano, akwai ƙungiyar limaman arewacin Najeriya wadda ita ma aka kafa ta da manufar samar da haɗin kai da fahimtar juna don amfanuwar al’ummar musulmin Arewacin Najeriya, kuma itama an nada shi a matsayin mataimakin shugaban ƙungiyar a shekara ta 2003 a jihar Kaduna, har zuwa wannan lokaci yana kan wannan matsayi kuma yana bada gudummawa yadda ya kamata.

4.1.2. GUDUMMAWAR SA A CIKIN SHA’ANIN HIDIMAR MASALLACI DA IBADA:
     i- Kasancewar sa a Matsayin ladanin Masallacin Maulan mu Shehu Ibrahim (Kaulaha):
     Kamar yadda ya gabata a babi na musamman a kan karatun tangimi, wanda hakan ta sa yake iya kwaikwayon kiran Sallah da irin salo da muryar Shehu Nazir (Ɗan Maulanmu Shehu Ibrahim Nyass), wanda har ta kai a wani lokaci da Shehu Nazir yayi tafiya, kuma wanda zai yi kiran Sallar a Madadin sa (Mbai Yasin) bai zo ba har lokacin Sallar yayi (Ranar Juma’a), a inda Malam da kansa ya ce zai iya kiran Sallar, kuma yayi kiran Sallar a gaban Maulanmu Shehu Ibrahim Nyass a shekara ta 1973 wanda hakan ya farantawa Shehu rai sosai, kuma daga wannan lokaci ne bayan Shehu Nazir ya dawo ya naɗa shi a matsayin wakilin sa wanda zai dinga yin kiran Sallah a Masallacin Shehu dake Madinatu Kaulaha wanda Malam shine dan hausawa na farko da ya fara samun wannan matsayi kuma su a can ana bawa masu kiran Sallah matsayi da daraja da mukami, ba kamar a sauran garuruwan na hausawa ba, babbar shaidar da za ta sa ka yarda cewar suna bawa kiran Sallar matsayi shine, kasancewar Sarkin garin Madinatu Kaulaha shima aikin sa kenan kafin girma ya kama shi, wanda bayan da ya tsufa sai aka bawa Shehu Naziru wannan matsayi na kiran Sallah, kuma har Malam yake wakiltar sa idan ba ya nan.
     ii- Kasancewar sa a Matsayin Ladanin Masallacin Shaikh Muhammadu Rabi’u (Kano):
     Malam Bayan dawowar sa daga Kaulaha, zuwa gida Najeriya, ya cigaba da bada gudummawa ga addini kamar yadda muka bayyana a baya (cikin babi na uku), kuma har a Shekara ta 1984, lokacin da Khalifa Shaikh Ishaƙa Rabi’u ya gina Masallacin Juma’a a unguwar goron dutse (Jihar Kano), ya shaida wa Malam Mudi Salga cewar yana Sha’awar bada tasa gudummawar ta ladanci a Masallacin kasancewar, shine Masallacin Juma’a na farko na ‘yan Tijjaniyya a Kano, kuma haka aka yi, a inda Malam ya zama ladanin masallaci, kuma ya kawo wa masallaci tsare-tsare kasancewar sa na wanda ya zauna a garin Kaulaha, kuma ya ga yadda ladani yake da mahimmanci da kuma yadda suke tsara sha’anin gudanar da masallaci cikin tsari mai ban sha’awa kamar yadda wannan bayanin ya zo a baya (Babi na uku).
     iii- Kasancewar sa a Matsayin Na’ibin Masallacin Shaikh Muhammadu Rabi’u (Goron Dutse, Kano) a shekara ta 1993 :
     A lokacin da Malam yake a matsayin ladanin Masallacin Shehu Muhammadu Rabi’u, mutane da dama sun tabbatar da cewar shi Mutum ne mai ilimi da gogewa, kuma hatta mai girma Halifa Mal. Ishaƙa Rabi’u da kansa yana mamakin irin kwazon sa kuma yana yaba masa, har zuwa lokacin da buƙata ta taso ta naɗin sabon na’ibin Masallaci kuma Khalifa Shaikh Ishaƙa Rabi’u tare da sauran manyan Malaman Ɗarikar Tijjaniyya na Jihar Kano suka amince da cewar Malam Muhammad Nasir Adam shine ya fi cancanta da wannan matsayi, kuma aka umarce shi da ya kawo kansa a nada shi a matsayin na’ibin wannan Masallaci na Shaikh Muhammadu Rabi’u a shekara ta 1993, wanda Shehu Abdullahi Nyass (Dan Maulanmu Shaikh Ibrahim Nyass) ne ya naɗa shi, kuma zaman sa a wannan muƙami na Na’ibi ya nuna ƙwazo da himma, a inda yake wakiltar Liman Malam Ashiru, idan baya nan, wanda a sakamakon haka ne har ya samu damar ƙirƙirar huɗubobi har guda bakwai (7), wanda a wancan lokaci, samun Limamin da yake da yawan huɗubobi, kamar haka abin a yaba masa ne, ballantana ace Na’ibi wanda bai kai matsayin limami ba, wannan yana ɗaya daga cikin ɗalilai da suka sa aka ga cancantar sa, aka sake daga likkafar sa zuwa matsayin Babban Limamin Masallacin Juma’a na Masallacin Shehu Ahmadu Tijjani dake a Unguwar K/Mata Jihar Kano.
     iv- Kasancewar sa a Matsayin Babban Limamin Masallacin Shaikh Ahmadu Tijjani, K/Mata Kano ashekara ta 1996:
     Manyan Malaman Ɗariƙar Tijjaniyya tare da Khalifa Shaikh Ishaƙa Rabi’u sun zauna don yin shawara akan wanda ya dace a naɗa shi a matsayin Limamin Masallacin Shaikh Ahmadu Tijjani wanda aka gina shi a shekara ta 1996, kuma suka yanke shawara akan cewa Malam Muhammad Nasir Adam shine wanda ya cancanta a naɗa shi a wannan matsayi, kuma bayan an naɗa shi, aka buɗe wannan Masallaci, wanda ya buɗe wannan massalaci shi ne marigayi mai martaba sarkin Kano Alh. Dr. Ado Bayeyo, Malam ya soma Salla a wannan masallaci da hudubar maulan mu sheikh Ibrahim Nyass don neman albarka kuma kamar yadda aka faɗa a baya cewar daga wannan juma’ar Malam ya ci alwashin cewar da yardar Allah sai ya shekara bai maimaita huɗuba ba, a inda Allah ya cika masa wannan buri nasa kuma ya samu damar ƙirƙirar huɗubobi na Sallar juma’a sama da Sittin da shida (66),masu bangarorin bayanai daban daban sannan ya haɗa su da hudubar daurin aure da ta raɗin suna da sauran su, ya mayar da su littafi kuma ya saka masa suna Almufid Lilkudaba’i Wal Murshidah, wannan littafi ya samu karɓuwa sosai a wurin Malamai da limaman Juma’a da Malamai masu karantarwa a manyan Makarantu da masu wa`azi, sannan Malam ya samu damar yaɗa wannan littafi a duniya, bugu da ƙari an buga shi har sau biyar a lokuta daban daban tun daga sanda aka wallafa shi a shekara ta 1999 zuwa yau, don haka, wannan gagarumar gudummawa ce abar alfahari kuma mai muhimmanci ga al’umma.
     v- Ƙirƙiro Takardar Shaidar Ɗaurin Aure ga Ma’aurata da sababbin shiga musulunci:
     Malam ya daɗe yana son samar da wannan takardar shaida, saboda yadda zamani ya juya kuma, abubuwa da dama ana buƙatar wannan takarda don ta zama shaida da za ta bawa ma’aurata, musamman mata damar samun sassauci da kima a cikin waɗansu al’amura, misali: Aikin khidimar ƙasa, wanda in mace tana da takardar shaidar aure ana ɗauke mata zama ko kwana a cikin sansanin ‘yan yiwa ƙasa hidima na wani lokaci. Haka kuma yana da amfani a sauran ƙasashen duniya, wanda basa yarda da mutum ya je da mace, yace matar sa ce har sai sun ga takardar shaida wanda daga ciki akwai wani daga cikin mutanan Malam wanda ya je ƙasar amurka tare da matar sa, kuma ya bugo wa Malam waya cewar yana buƙatar wannan takarda, kuma Malam ya sa aka fitar masa da ita, aka aikawa wannan Mutum, kuma Malam yana sa ran nan gaba, za’a ga duk ma’auratan da aka ɗaura musu aure a Masallacin sa, sun mallaki wannan shahadar.
     vi- Samar da Sabon tsarin Shugabanci a Masallaci: Malam ya tsara wa Masallatan sa na goron dutse da na k/mata tsarin shugabanci hawa huɗu, kamar haka:
     1. Babban Limami
2. Na’ibin Babban Liman
3. Liman Ratibi
4. Na’ibin Liman Ratibi
• Aikin Babban Liman: shine jan Sallar Juma’a da sauran Salloli da hidimar ɗaurin aure da jagatanatan santar taruka da majalisai waɗanda Masallaci yake shirya wa.
• Na’ibin Liman: shine wanda yake gabatar da dukkan aiyyukan da Liman yake gabatarwa idan Liman baya nan.
• Liman Ratibi: shine yake da alhakin gabatar da Salloli biyar na rana, sannan yana wakiltar Babban liman a cikin sha’anin Masallaci idan Na’ibi baya nan.
• Na’ibin Liman Ratibi: Shi kuma Wakili ne na Liman Ratibi a salloli biyar, a lokacin da baya nan, shi ne zai ja ragamar masallaci, kuma in ya kasance Babban Liman da Na’ibin sa da Liman Ratibi basa nan shine a Matsayin wanda zai ja Sallah.
Idan muka yi duba ga wannan tsari zamu ga cewar an yi shine ta yadda zai yi wuya a ce sha’anin jagoranci a Masallaci ya samu karaya, kuma wannan tsari shine irin sa na farko a Jihar Kano wanda Malam ƙirƙiro shi a Masallatan sa, kuma daga nan Masallatai da dama suka kwaikwaya, a halin yanzu Allah ne kaɗai ya san yawan Masallatan da suke akan wannan tsari. Wannan ma babbar gudummawa ce ga addini, muna fatan Allah ya karɓa, ya sa a mizani.

2.1.3. GUDUMMAWAR SA A ƁANGAREN MAKARANTUN ISLAMIYYA DA SAURAN MANYAN MAKARANTU (JAMI’O’I) NA ƘASASHEN DUNIYA:
     Malam kamar yadda aka ji a baya cewar bayan ya dawo daga ƙasar Sinigal, gudummawa ta farko da ya fara bayarwa ita ce kafa Makarantun addini tare da yi musu ingantaccen tsarin gudunarwa don karuwar al’ummar musulmi, daga cikin waɗannan makarantu da ya samu damar kafawa sun haɗar da:
     i. Makarantar Sabi’lulfalahi:
     Wannan Makaranta an assasa ta a Unguwar cikin birni unguwar manladan Kano, kuma Malam ne ya tsara mata tsarin gudanarwa sannan ya raɗa mata suna, kuma ya jagorance ta daga shekarata 1974 zuwa 1977. kuma makarantar tana da bangaren yara ‘yan islamiyya da ‘yan mata, sannan kuma akwai ɓangaren samari da matasa waɗanda suke gabatar da karatun su da daddare, kuma abin sha’awar shine yadda ake gabatar da karatu cikin harshen larafci zalla, a bangaren yamma da dare bayan `yan islamiyya sun tashi (10-12 na dare), don daliban su samu gogewa a cikin harshen larafci tare da kware wa.
Daga cikin ɗaliban wannan Makaranta akwai irin su: Mal. Yahaya Bashir Dodo Sanka,Alh. Malam (Ɗan Mal.Mudi) da Mustafa, (Ɗan Alh. Talata) da Ibrahim ɗan Mal. Bashir Dodo da Sani ɗan Alh. Yahuza mai goro da kuma Hadiza `yar Alh. Inuwa da dai sauran su.
     ii. Makarantar Nahda:
     Malam ya kasance shine shugaban wannan Makaranta, ya kafa ta a shekara ta 1975, a unguwar Gwammaja (Kukar `yan caca), karamar hukumar Dala a Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Shaikh Mal. Mudi Salga, kuma wannan makaranta islamiyya ce (Firamare) wadda ake gabatar da karatu safe da yamma, kuma ana koyar da Alƙur’ani da larabci da sauran darrusan addini da na boko. Bugu da ƙari ita ma wannan makaranta ta yaye ɗalibai masu yawan gaske tun daga lokacin da aka kafa ta zuwa yau, ga wasu kaɗan daga cikin su kamar haka: Sharif Ahmad, Ali Ahmad, Hadi Tijjani Ma`azu, Rayyashi Atiku Sanka, Alh. Salihu Labaran, Aliya Kabiru Salga, Abdurrahim M.Mudi Salga, Alh. Ummaru, Yusi M.Nura Arzai, Mal. Aminu Umar, M. Sukairaju Arzai, M.Danliti Arzai, M.Abubakar Arzai, M.Nura Khaladu, Isma`il, Auwalu Hussaini, Muttaƙa Sharif,da Tijja Lawan (na gidan rediyan Eɗpress kano). Da sauran su.
     iii. Makarantar Shaikh Tijjani Usman Z/Bare Bari:
     Wannan makaranta sakandare ce, wadda aka kafa ta ita ma a unguwar gwammaja kukar `yan caca, sannan ita ma tana ƙarƙashin ƙungiyar munalzamatu fitiyanul Islam wadda Shaikh Mal. Mudi Salga yake shugabanta, an kafa wannan makaranta a shekara ta 1977, a inda Malam ya kasance shine wanda ya assasa ta kuma ya tsara mata manhaja tare da rada mata suna, shi da Mal. Laminu Umar. Duk da kasancewar sa shugaban makarantar Nahda, amma hakan bai hana shi kula da ita wannan makarantar sakandare ba, a matsayin sa na mataimakin shugaban makaranta (Ɓice Principal), kaɗan daga cikin ɗaliban sa sun haɗar da: M. Murtala Shehu Abulfatahi, Sule Ya`u Sule, da dai sauran su dubbai maza da mata.
    
     iv. Makarantar Shaikh Muhammadu Rabi’u:
     Wannan Makaranta Malam ne ya assasa ta a shekara ta 1984, a unguwar goron dutse, bayan Khalifa Shaikh Mal. Ishaƙ Rabi’u ya gina masa gida a unguwar goron dutse kuma ya koma unguwar ya tare, sai ya bawa Khalifa Shaikh Mal. Ishaƙa Rabi’u shawarar cewa ya kamata a samar da makaranta ta addini (Islamiyya) don yara ‘yan unguwa su samu ilimin addini a kusa tare da haddar, Alƙur’ani, kuma Khalifa Mal. Ishaƙa Rabi’u ya yarda, sannan ya miƙa masa agamar komai da komai na sha’anin ginin makaranta da tsare-tsare, kuma bayan an kammala ginin makaranta, sai ya raɗa mata suna “Shaikh Muhammadu Rabi’u Littahfizul Ƙur’an Waddirasatul Islamiyya” A idan aka fara karatu, lokacin Khalifa Mal. Ishaƙ Rabi’u baya nan, bayan ya dawo sai ya tarar makaranta har ta kankama, abin gwanin sha’awa, kuma ya tambayi Malam cewar nawa ɗalibai suke bayar wa na kuɗin makaranta, sai yaji yayi kaɗan, sai yace “ai ya kamata a saka abinda ko da bama nan makaranta ba za ta ruguje ba, kuma kai ma, in aka yi haka sai ka fi samun damar biyan malaman ka cikin sauƙi” haka kuwa aka yi, a inda aka sanar da iyayen yara, kuma suma suka amince suka ƙara, makaranta ta tsaya da ƙafafunta, sannan shima Halifa yana bata taimako na musamman har zuwa wannan lokaci.
     v. Malam ya kafa makarantar Islamiyya a Jihar Katsina (ƙofar ƙwaya) mai suna Sabilul falahi a gidan Sharif Abba Abu Rafin daɗi:
     A sakamakon zaman da Malam yayi a Katsina lokacin da ya koma don yin karatun zamani (don ya samu takardar shaidar Malanta), ya assasa wannan Makaranta mai suna a sama a matsayin nasa gudummuwa don ɗaukaka addinin Allah a duk inda bawa Musulmi ya sami kansa har yanzu wannan makaranta tana nan tana cigaba da gudana.
     vi. Kasancewar sa a Matsayin Wakili, a Jami’ar Saye Wadda take a Kasar Nijar:
     Malam an zaɓe shi domin ya kasance ɗaya daga cikin wakilai na majilisar zartarwa ta Jami’ar saye wadda take a ƙasar Nijar (Sanate Member) kuma wannan takarda da ake gani a ƙasa ita ce shahadar da wannan Jami’a ta aiko masa da ita kafin karɓar wannan matsayi. Jami`ar ta kasance ƙarƙashin OIC. Jidda Saudi Arabiya;
    

     vii. Kasancewar sa wakili a Jami`ar Ifriƙiyya ta ƙasar Sudan:
     Malam ya kasance wakili a wannan Jami`a, wannan takarda da take a ƙasa ita ce shahadar tabbatarwa, da wannan jami`a ta aikowa Malam kamar yadda kuke ganin ta;
    

     viii. Kasancewar sa a Matsayin Wakili kwamitin sha`anin addinin Musulunci na ƙungiyar O.I.C mai hedikwata a Jidda ta Ƙasar Saudi Arebiya:
     Wannan ƙungiya ta ƙasar Saudi Arebiya, itama ta zaɓi Malam a matsayin ɗaya daga cikin wakilan ta a kwamitin sha`anin addinin musulunci, wannan takarda da take ƙasa ita ce shahadar da wannan ƙungiya ta aiko masa da ita a lokacin da ta zaɓe shi a wannan muhimmin matsayi;
    
     Jidda ta Ƙasar Saudi Arebiya:
     Wannan ƙungiya ta ƙasar Saudi Arebiya, itama ta zaɓi Malam a matsayin ɗaya daga cikin wakilan ta a kwamitin sha`anin addinin musulunci, wannan takarda da take ƙasa ita ce shahadar da wannan ƙungiya ta aiko masa da ita a lokacin da ta zaɓe shi a wannan muhimmin matsayi;

2.1.4. Gudummawar sa ga Sha’anin Harkar Lafiya:
     Sha’anin harkar lafiya wani babban ɓangarene da addinin musulunci ya bawa fifiko da muhimmanci a rayuwar ɗan Adam, kuma Allah Maɗaukakin Sarki ta Harshen Annabin sa ya ce damu mu ribaci lafiyar mu kafin rashin lafiyar mu (wajen aikata ayyukan alheri).
A sakamakon wannan dalili ne ya sa Malamai a matsayin su na magada Annabawa suka shiga bada irin tasu gudummawar a sha’anin harkar lafiya ta fuskoki da dama, daga cikin irin wannan ne shima Malam ya ke bada tasa gudummawar wanda har gwamnatin tarayya ta na saka shi a cikin wasu kwamitoci na harkar lafiya na ƙasa sannan tana gayyatar sa taro, don ya bada tasa gudummawar. Wannan takarda mai zuwa tana nuna haka;

     i. Kasancewar sa Wakili a kwamitin Yaƙi da Cutar Foliyo na Jihar Kano (Ambasaddor of Polio):
     Wannan matsayin an bawa Malam shi kuma an ɗora musu nauyin wayar wa da al’umma kai dangane da illar cutar foliyo wadda aka fi sani da (cutar shan inna). Sannan an ɗora musu alhakin sanar da al’umma halarcin yin wannan rigakafi a addini bugu da ƙari da kuma sanar dasu cewa Allurar ba ta da illa ga rayuwar al’umma kamar yadda ake yaɗa jita-jita, kuma cikin yardar Allah an samu nasarori.
     ii. Kasancewar sa Wakili a Kwamitin Yaƙi da cutar shan inna a Najeriya:
     Bayan Malam ya zauna a matsayin Wakili a kwamitin yaƙi da cutar shan inna na Jihar Kano, (Polio Ambassador). Malam ya samu ƙwarin gwiwar cigaba da shiga cikin sha’anin yaƙi da cutar, a sakamakon zuwan Sayyidi Hassan Ɗan Sayyidi Aliyu Sisa, wanda ya ƙarfafa musu gwiwar cewar lallai su tsaya tsayin daka don ganin an yaƙi wannan cuta,wannan shine babban dalilin da ya ƙarfafa masa gwiwa.
     iii. Alaƙar sa da Ƙungiyoyi na Duniya masu bada Gudummawa a kan sha’anin Kiwon Lafiya:
     A sakamakon shigar sa sha’anin bada gudummuwa ga sha’anin harkar lafiya, ta fuskar wayar da kan al’umma, ya samu gayyata daga manyan ƙungiyoyin duniya masu kula da wannan bangare, sannan ya samu damar shiga kwamitoci da dama a wannan banagre. Daga cikin waɗannan ƙungiyoyi akwai: UNICEF, ROTARY, WHO da sauran su, bugu da ƙari akwai ma’aikatar lafiya ta ƙasa, Malam ya samu damar kasancewa ɗaya daga cikin Malamai da suke da kyakkyawar alaƙa da fahimtar juna a inda duk abin da ya taso ake buƙatar shigowar Malamai suna neman sa daga lokaci zuwa lokaci, akwai takardun gayyata masu nuna haka.

     Gabatar da shirye shirye a Kafafen yaɗa Labarai akan sha’anin harkar lafiya:
     Malam yana gabatar da shiri na musamman a wasu daga cikin kafafan yaɗa labarai na Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya tare da sauran wakilai na waɗansu bangarori waɗanda suka haɗar da likitoci da masu sarautar gargajiya da yan jaridu, sannan shi kuma ya kasance wakili a inda suke gabatar da shiri na kai tsaye don faɗakarwa ga al’umma akan abinda ya shafi kula da harkar lafiya daga cikin kafafen yaɗa labarai da Malam yake gabatar da shirye shirye akwai: Rediyan Kano, Rediyan Firidom, Rediyan Firamid, Rediyan Eɗpiress da Rahama FM Kano da sauran su.

TAFIYE-TAFIYEN MALAM 5.1 TAFIYE-TAFIYE DON NEMAN ILIMI
     Da farko shi malam ya kasance tun yana da ƙananan shekaru ya fara tafiye-tafiye, domin neman ilimi, a inda mahaifinsa ya fara kai shi garin Dankar wanda yake a Jihar Katina, a shekara ta 1957, kuma an sake ɗauko shi daga wannan gari zuwa cikin garin Katsina ƙofar ‘yan daka, a inda ya ƙarasa karatun sa a can har ya sauke Alƙur’ani, kuma a wannan tsakani Malam sun tafi tare da mahaifinsa zuwa Ƙasar Sinigal garin Madinatu Kaulaha a shekara ta 1960, kuma ya zauna tsawon shekaru bakwai, sannan ya dawo Najeriya ya sauka a Ƙauran-Namoda, (garin Tingar Hilani) a shekara ta 1967 zuwa 1968, sannan ya yi noma ya samu kuɗin mota, ya kuma sake biya wa kansa, ya koma ƙasar Sinigal, garin Madinatu Kaulaha, a inda ya cigaba da karatun sa kamar yadda yake yi kuma ya shafe shekaru shida a wannan komawar ta biyu (1968-1974) in aka haɗa za mu ga cewa ya zauna tsawon shekara goma sha uku (13) a Madinatu Kaulaha. Daga nan malam ya zauna a kano a matsayin ɗalibi, a inda ya yi karatu a wurin malamai da dama.
     5.2 TAFIYE-TAFIYE DON WA’AZI A CIKIN GIDA NAJERIYA
     Bayan al’amuran sa na hidimtawa addini sun faɗaɗa daga matsayin malamin makaranta zuwa mai wa’azi, sai ya kasance ƙarƙashin ƙungiyar (Fitiyanul Islam) ɗaya daga cikin malaman Ɗariƙar Tijjaniyya da suke zuwa wa’azi da tarurruka jiha-jiha, wanda a sakamakon haka ya samu damar zuwa baki ɗayan jihohin ƙasar nan tamu ta Najeriya guda talatin da shida (36). A shekarar 1985, lokacin da ya zama sakataren cibiyar addinin Musulunci ta Sheikh Muhammad Ishaƙa Rabi’u, tafiye-tafiyen sa sun ƙaru, saboda wannan matsayi da khalifa Sheikh Ishaƙa Rabi’u ya bashi, kuma sai ya kasance duk wani taimako da Khalifa Sheikh Ishaƙa Rabi’u zai bayar, shi ne ya ke zuwa ya kai wannan saƙo, musamman taimakon da ya shafi harkar addini, wajen ginin masallatai da makarantun Islamiyya da taimakawa makarantun allo da harkar Musabaƙar Alƙur’ani da ɗaukar nauyin karatun ɗalibai a cikin g ida da wajen Najeriya da sauransu.
     5.3 TAFIYE-TAFIYENSA ZUWA ƘASASHEN DUNIYA
     Malam ya yi tafiye-tafiye da dama zuwa sauran ƙasashe waɗanda suka haɗar da ƙasashen yankin Afrika da Asiya da kuma Turai. Wanda a mafi yawan lokaci yakan je waɗannan ƙasashe a sakamakon gayyata da ya samu don halartar taro da aka shirya shi a kan addini.
Daga cikin ƙasashen da malam ya samu damar ziyarta sun haɗar da:- 1. Nijar
2. Gana
3. Togo
4. Cadi
5. Gambiya
6. Sudan
7. Mortaniya
8. Moroko
9. Tunisiya
10. Libiya
11. Sinigal
12. Ingila
13. Jamus
14. Misra (egypt)
15. Dubai
16. Maida
17. Sybros
18. Sirilanka
19. Fakistan
20. Koddebuwa
Daga cikin waɗannan ƙasashe da Malam ya samu damar halarta akan sha’anin addini akwai ƙasar Moroko kamar yadda muka faɗa a baya, wadda kasancewar ta ƙasa ce ta Shehu Ahmadu Tijjani, kuma ban da ziyara da ake kaiwa, akwai tarurruka masu yawa da malam ya samu damar halarta, daga ciki akwai taro wanda aka shirya na ‘yan Ɗariƙar Tijjaniyya na duniya, kuma dukkanin manya-manyan malamai na Ɗariƙa na duniya da yawan su sun samu damar halartar wannan taro, sannan akwai taron da wani babban malamin Ɗariƙar Ƙadiriyya ya shirya kuma ya gayyaci malam, shi ma a ƙasar Moroko aka yi kuma malam ya samu dama ya gabatar da jawabi a wurin wannan taro a inda ya ƙara bayyana musu cewa Ɗariƙun Sufaye, babu karo a tsakaninsu, kuma babu saɓani tsakanin Sheikh Ahmadu Tijjani da Sheikh Abdulƙadir Jilani, ballantana tsakanin mabiyan su, saboda haka duk wani saɓani da aka samu an ƙirƙire shine, daga baya don cimma wata buƙata ta ƙashin kai, amma ba haka abin yake ba, saboda haka, idan Batijjane yaje taro don nuna girmamawa ga wani Baƙadire, wannan ba komai bane, kuma malam ya cigaba da shaidawa mahalarta taron cewa mu ‘yan Tijjaniyya, muna ganin girman ‘yan uwantaka kuma ba ma ƙaunar ace mun muzgunawa wani ɗan Adam a rayuwa.
     Bayan haka, akwai taro wanda Sarkin Moroko (Muhammadus Sadis) ya shirya shi na malaman Afrika, kuma aka aiko wa malam takardar gayyata, a matsayin sa na ɗaya daga cikin malaman da aka zaɓa daga Najeriya, an shirya wannan tsaro ne musamman don haɗin kan malaman Afrika.
     Daga ƙasar Moroko sai ƙasar Sudan wadda malam ya kan wakilci Khalifa Sheikh Ishaƙa Rabi’u a inda yake kai ɗalibai ‘yan Najeriya don su yi karatu ƙarƙashin cibiyar addinin Musulunci ta Sheikh Muhammadu Rabi’u wacce Khalifa Sheikh Ishaƙa Rabi’u yake ɗaukar nauyi. Bayan haka Jami’ar Ifriƙiyya ta ƙasar Sudan ta zaɓi Khalifa Sheikh Ishaƙa Rabi’u a matsayin wakili a majalisar zartarwa (Sanate member), wanda a sakamakon haka, malam ya je Sudan sau da dama.
     Daga nan, akwai ƙasar Makkah da Madina, wadda a matsayin ta da kasancewar ta alƙiblar Musulmin duniya, kuma dukkan wani musulmi mai imani ba ya wadata ga barin ta, wannan ya sa malam ya je ƙasar Makkah sau da dama don yin ibada da kuma garin Madinatul Munawwara don ibada da ziyarar ƙabarin Annabi (SAW). Da fatan muma Allah ya kai mu, kuma ya sake kai mu ba adadi, amin.
     Sannan akwai alaƙa ta rabiɗa, wadda ake zama tare da malaman duniya a ƙasar Saudiyya don tattaunawa akan sha’anin addinin Musulunci, wadda shi ma malam yana cikin waɗannan malamai, sannan akwai ƙungiyar O.I.C wadda ita ma malam ɗaya ne daga cikin malaman da suke a matsayin wakilci a cikin kwamitin sha’anin addinin Musulunci da rayuwa, kuma sun shafe shekaru da dama a cikin ta. Bugu da ƙari malam yana jagorantar kai ɗalibai, wanda Khalifa Sheikh Ishaƙa Rabi’u ya ɗauki nauyin karatun su, kuma yana samun karramawa sosai daga wurin hukumar ƙasar Saudiyya.
     Daga nan sai ƙasar Misra (Egypt) wadda ita ma akwai irin waccan alaƙa ta kai ɗalibai, da kuma taro da suke gabatarwa daga lokaci zuwa lokaci tare da Sheikh al-Azhar, a Jami’ar Azhar ta ƙasar Misra.
     Sannan ƙasar Libiya, malam ya samu gayyata a karo da dama, sannan ya halarci taruka na addini kuma a irin waɗannan tarukan ya samu damar gabatar da ƙasidu da makala da ya rubuta masu alaƙa da maƙasudin taron da ya halarta, kuma alaƙar sa da wannan ƙasa tsohuwar alaƙace tun lokacin marigayi Mu’ammar Gaddafi (tsohon shugaban ƙasar Libiya).
     Daga nan sai ƙasar Tunusiya, wadda ita ma malam yana da alaƙa da wannan ƙasa, kuma akwai fahimtar juna tsakanin sa da malaman Jami’ar Ƙirawan.
     Bayan haka, sai ƙasar Nijar wadda ita ma akwai waccan sananniyar alaƙa da take haɗa shi da sauran ƙasashen duniya, ta kai ɗalibai karatu, haka kuma, yana da muƙami na wakili a majalisar zartarwa ta Jami’ar Saye, wadda take ƙasar Nijar (sanate member), sannan akwai alaƙa ta da’awa da Maulidai da kuma alaƙa ta zumunci, wadda idan mai karatu bai manta ba mun faɗa a babi na ɗaya (1) cewar: mahaifin Malam (Shehu Malam Adamu) a sakamakon yawan neman ilimi da yaɗa addini da yayi da kuma tafiya da yayi zuwa ƙasar Saudiyya a ƙafa ta sa ya samu damar ƙulla alaƙa tsakanin sa da mutanen ƙasashen Afrika da dama, daga ciki har da ƙasar Nijar da Sudan wadda har a yanzu haka, akwai ‘ya’ya da ‘yan uwa a can, kuma malam yana samun dama daga lokaci zuwa lokaci yana ziyartar su.
     Sai ƙasar Gana, wadda malam ya samu damar amsa gayyata da suka yi masa a lokuta da dama, daga ciki akwai Maulidai wanda ya gabatar da jawabi ya kuma halarci wasu taruka waɗanda suka shafi addini.

TSARIN RAYUWA DA AL’AMURAN CIKIN GIDA
6.1 KYAKKYAWAR MU’AMALARSA GA AL’UMMA
     Kamar yadda mai karatu ya karanta a baya, malam jajirtaccen mutum ne tunyana ɗalibta, zuwa lokacin da ya zama shugaban makaranta, mai hidimar masallaci kuma mai wa’azi, wannan tsari ne na rayuwa mai kyau, yayi mu’amala da mutane da dama a ciki da wajen Najeriya. Daga cikin irin waɗannan mutane akwai manyan shuwagabannin al’umma da manyan malamai da sarakuna da attajirai da ma’aikatan gwamnati da almajirai da ƙungiyoyin al’umma da sauran su. Wannan mu’amalar da take tsakanin sa da waɗannan ɓangarori na al’umma ta sa tsarin rayuwarsa ya kasance abin sha’awa, musamman idan muka yi la’akari da yadda yake da kyakkyawar mu’amala da kowa da kuma wayewa da sanin halayyar mutane ta yadda fahimtarsa ga al’amuran rayuwa ya kasance mai faɗi, a koda yaushe idan za ka saurari lafazin sa za ka ji cewar lallai kana magana da wanda ya san abin da yake yi kuma yake da kyakkyawar fahimta da sani a cikin abin da kuke tattaunawa.
     Malam a koda yaushe ba ya rabo da Jama’a musamman a gidan sa, wanda ko tafiya yayi da zarar an ji labarin ya dawo za’a dinga zuwa don a samu damar tattaunawa da shi. A tsarin malam ya kasance da safe bai fiya ganin mutane ba saboda shima yana fita zuwa ofishin sa, ko kuma wani taron da aka gayyace shi, sannan da la’asar bayan ya dawo gida yana ganawa da mutane har zuwa magariba, amma ɗaya daga cikin abinda na yi la’akari da shi dangane da malam shine tarin baiwa da Allah ya bashi na iya sauraron magana idan ana yi masa, musamman idan an kawo masa wata matsala ko husuma tsakanin wasu mutane ko akan rikicin ginin Masallaci ko Makaranta ko rabon kuɗi da sauransu, ya kasance yana sauraron mai magana amma yana tantancewa, ba kawai maganar yake ji ba, so yake ya fahimci ainihin ta inda matsalar ta samo asali ko wane ne ya shigo da son zuciya, kuma koda an ɓoye masa wani abu ba’a gaya masa ba za ka ga a bayanin sa ya kawo dalilan da suka sa matsalar ta faru a ciki har da abin da aka ɓoye masa saboda kaifin fahimtarsa.
     6.2 ALAƘAR SA DA SHUGABANNIN AL’UMMA ‘YAN SIYASA
     Malam a matsayin sa na mai-wa’azi, wanda wannan babban aiki ne na Annabawa wanda ya shafi faɗar saƙon Allah ga al’umma baki ɗaya, don haka alaƙarsa a matsayinsa na malami da shugabannin siyasa kyakkyawa ce, kuma bakin gwargwado yana kamantawa wajen faɗar gaskiya ga shugabanni komai ɗacin ta, sannan wannan gaskiya yana faɗa musu, a sirrance da kuma a bayyane saboda yin hakan sauke nauyin amana ce, wacce Allah ya ɗora musu.
     Sannan malam ba shi da jam’iyya ta siyasa domin shi ba ɗan siyasa bane, shi kowa ma nasa ne, amma ya kasance a shirye yake ya taimaki duk wanda Allah ya bawa mulkin jama’a da addu’a da shawarwari da kuma duk wani abu da zai sa al’umma su samu cigaba da wadata cikin kwanciyar hankali, daidai gwargwadon ikon sa tare da kiyaye matsayin rigar malanta.
     6.3 ALAƘAR SA DA SARAKUNAN GARGAJIYA
     Malam a matsayin sa na malami mai wa’azi wanda wannan matsayi ne da yake bawa malamai damar faɗa a ji a cikin a’umma, saboda darajar ilimi, hakan ta sa yana da alaƙa ta kai tsaye da sarakunan gargajiya, musamman masarautar kano wadda yake da alaƙa da ita tun tsawon shekaru masu yawa, kuma a lokuta da dama ana gayyatar sa cikin sha’anin masarauta musamman wanda ya shafi addinin Musulunci da kuma wasu muhimman tarurruka na musamman. Daga cikin irin waɗannan tarurruka da fadar Kano take gayyatar malam akwai sha’anin ganin wata da wasu kwamitoci na musamman kamar kwamitin bikin cika shekaru hamsin (50) a kan mulki wanda marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Dr. Ado bayero ya yi a shekara ta ...... Banda wannan sai jawabi a wajen taron Zikirin Shekara-shekara, wanda malam yake gabatarwa, sannan sai fassarar (Tafinta) bayanin manyan baƙi waɗanda ba sa jin hausa sai Larabci, wanda baki ɗaya ake gabatarwa a fadar masarautar Kano duk shekara. Banda masarautar kano malam yana da kyakkyawar alaƙa da sauran masarautu na Arewacin Najeriya tun daga kan fadar sarkin Musulmi da take a Sokoto har zuwa kan sauran masarautu manyan su da ƙananan su, har ma akwai masarautar Batsari da take a Jihar Katsina, wadda ta bawa malam sarautar “Shetiman Batsari” wanda wannan sarauta, sanannen abu ne ba a bayar da ita sai ga manyan malamai.
     6.4 ALAƘARSA DA MALAMAI
     Sanannen abu ne ga duk wanda ya san malam cewar shi Ɗan Ɗariƙar Tijjaniyya ne kuma ɗaya ne daga cikin almajiran Shehu Ibrahim Nyass, amma duk da haka malam yana da kyakkyawar alaƙa tsakanin sa da sauran malamai na sauran Ɗariƙun da muke da su a ƙasar mu, sannan banda ‘yan ɗariƙar har da ‘yan izala, waɗanda suma suna yabon sa domin shi yana da fahimtar cewar kowa yayi abin da ya kamata a cikin addinin sa kuma ya tabbatar da duk abinda ya aikata ba ra’ayin sa ba ne, kuma ba gani yayi ana yi shima yayi ba a’a, sai dai mutum ya tabbatar ya nemi sani a cikin addinin sa, sannan yayi aiki da abinda malamansa suka ɗora shi akwai, matuƙar ba saɓon Allah bane, domin malamai su e magada Annabawa, kamar yadda yazo a hadisi.
     A sakamakon tafiye-tafiye zuwa ƙasashen duniya na larabawa, malam ya samu ƙulla alaƙa da malamai da dama, waɗansunsu kuma sun haɗu ne wajen wani taro sau ɗaya ko sau biyu, daga cikin irin waɗannan manyan malamai na duniya akwai Sheikh al-Sudais babban limamin haramin Makkah, kuma babban limamin fatawa a ƙasar Saudiyya kamar yadda hoto mai zuwa yake nuna wa.
     Dangane da Malaman mu na nan gida Najeriya kuwa malam yana da kyakkyawar alaƙa da su matuƙa daga ciki akwai shugaban Ɗariƙar Tijjaniyya Khalifa Sheikh Ishaƙa Rabi’u wanda malam ya kasance hadimi a gare shi, sai Khalifa Sheikh Ƙaribullah shugaban Ɗariƙar Ƙadiriyya na yammacin Afrika da kuma Sheikh Sale Fakistan shugaban ƙungiyar Izala da sauran su.
     Malam a matsayin sa na muridin Shehu Ibrahim Inyass (RTA) ya kasance yana da kyakkyawar alaƙa da ‘ya’ya Maulanmu Sheikh Ibrahim (RTA) baki ɗayan su, sannan a duk lokacin da suka kawo ziyara Kano, shi ne yake yi musu hidima ta rakiya da kuma tafinta tsakanin su da shugabanni da kuma sauran al’umma a wurin majalisai da akan shirya idan sun zo, kuma idan ya je can ƙasar Kaulaha suna jan sa a jiki, kamar ɗan dangi a inda ya kan samu damar shiga hubbaren Shehu da kuma ɗakin kwanan sa su yi sallah tare da ‘ya’yan Shehu da sauran manyan muridai.

6.5 AL’AMURAN MALAM NA CIKIN GIDA
Malam yana da mata biyu (2) da ‘ya’ya goma sha huɗu (14).

6.5.1 ‘Y A’YAN MALAM (MAZA)
Malam yana da ‘ya’ya maza guda bakwai kuma baki ɗay ansu kowanne ya hau layi na neman ilimi da tsarin rayuwa ingantacciya. Amma dama hausawa na cewa barewa ba za ta yi gudu ba ɗanta yayi rarrafe, ga sunayen su da kuma matsayin da kowannen su ya taka a ilimi kamar haka:-

(1) Lauwali: Makaranci ne (hafizi) kuma yana karatun Lauya a ƙasar Sudan.
(2) Naziru: Ya gama Aminu Kano Commercial College, Kuma yanzu yana kasuwanci.
(3) Ibrahim (Shehi): Yana karatun P.H.D a Sudan akan Arabiya a Jami’ar.
(4) Aliyu Sisa: Shima makaranci ne (hafizi) kuma yana shirin shiga Jami’a.
(5) Tijjani: Shi ma makaranci ne (hafizi) yana shirin shiga Jami’a.
(6) Rabi’u: Makaranci ne yana karatun sakandare a Kwalejin Rumfa.
(7) Adamu: Shima yana karatun sa na Alƙur’ani a halin yanzu.

6.5.2 ‘YA’YAN MALAM (MATA)
Malam yana da ‘yaya mata guda bakwai (7) kamar haka:-

(1) Aisha: Ta yi H.I.S, yanzu haka tana cigaba da karatun ta a fannin lafiya.
(2) Hadiza: Ta sauke Alƙur’ani, kuma hafiza ce, ta yi karatun ta a makarantar haddar Alƙur’ani ta Goron Dutse ta gwammantin Jihar Kano, sannan yanzu haka tana aure a ƙasar Nijer.
(3) Nafisa: Ta yi karatun ta na Jami’a a Jami’ar Bayero.
(4) Ruƙayya: Ɗaliba ce a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar Aduwa ta Jihar Katsina.
(5) Halima: Ta yi karatun kiwon lafiya (nurse) a makarantar kiwon lafiya ta Asibitin kashi da ke Jihar Kano.
(6) Fatima: Ita ma ɗaliba ce wadda take ƙarasa haddar Alƙur’ani da Babbar Sakandare.
(7) Safiya: Ɗaliba a makarantar haddar Alƙur’ani ta ƙofar mata Kano.


    Waɗannan sune ‘ya’yan Malam guda goma sha huɗu (14) maza da mata. kamar yadda na faɗa a baya cewar Barewa ba za tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba, domin idan muka duba lay in da suke kai, za mu ga cewar layi ne na ilimi da karatun Alƙur’ani, kamar yadda shi ma magabatan sa suka ɗora shi akai, kuma bayanin haka ya gaba ta baya.
     Ta ɓangaren ganawa da jama’a a cikin gida malam yana da tsarin lokuta da yake zama a gida da iyalan sa, sannan yana da lokaci na ganawa da baƙi, wanda yake zama a buɗaɗɗen zauren gidan sa bayan sallar la’asar zuwa magariba, a cikin mu’amalar sa da baƙin sa. Na lura cewa malam yana da yawan fara’a ga wanda ya sani da waɗanda ma bai sansu ba, sannan ga tawali’u da girmama mutane.
     Ta ɓangaren sutura malam yana yawan saka suturu farare, sannan a kowanne lokaci shigar sa babbar riga ce da hula, kuma yana yawan saka hula ‘yar maroko, a lokuta da dama musamman ranar juma’a yanayin rawani sannan yana saka Alkyabba ya riƙe sanda, ya fita zuwa Masallaci, irin wannan shiga tana da tasiri wajen sakawa mutane ganin girman addinin, kwarjininsa a zukatan su, sannan an so ga duk wanda zai yi kira zuwa ga addinin Allah (wa’azi) to yayi shiga ta kamala sabo da tasirin da hakan yake da shi a wurin masu ganin sa, wannan wani sirri ne ga masu wa’azi, domin an samu cewa Imamu Abu Hanifa Allah yayi masa Rahama yana gaya wa malamai cewa “ku yi rawani mai girma sanna ku yalwata hannayen rigunanku domin kar a raina ilimi”.
     A ɓangaren abinci kuma, malam yana son shayi sosai, wannan ba ya rasa nasaba da zama da yayi a Kaulaha, kuma yana da gas da butar shayi ta silba wacce a kullum da yamma idan ya zauna ake dafa masa. A ɓangeren nishaɗi, babban abin da yake nishaɗantar da malam shi ne Zikiri musamman a cikin da’ira, sannan a waɗansu lokutan idan yana hutawa yakan kunna tsofaffin waƙoƙin larabawa yana saurara ko diwani yana sauraro kuma yana jan carbi, a waɗansu lokutan idan yana tare da wani masanin harshen larafci sukan tattauna akan balagar da waƙar ta ƙunsa da kuma sauran bayanai na ilimi wanda sai waɗanda suka yi zurfi a harshen larafci ne za su gane.